Kwastam ta kama manyan motoci 15 na kayan abinci a Sakkwato

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama wasu manyan motoci guda 15 da suka dauko kayan abinci a Jihar Sakkwato.

Kwastam ta kama manyan motoci 15 na kayan abinci a Sakkwato

Kwastam

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama wasu manyan motoci guda 15 dauke da kayan abinci a Jihar Sakkwato.

Ofishin hukumar na shiyyar Sakkwato ya ce jami’ansa sun kama motocin ne a wani bangare na aikin hana fasa kwaurin kayan abinci, lamarin da take zargin ya ta’azzara tsadar kayayyaki a Najeriya.

Kakakin hukumar a jihar, Abubakar Chafe, ya ce jami’an sun sanya alamar tambaya a kan motocin ne saboda yawan amfanin gonar da suke dauke da su.

Jami’ain ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa an kama motocin ne a kan hanyar Gwadabawa zuwa Illela.

Ya ce a halin yanzu hakan manyan motocin suna hannun hukumar kuma an fara bincike don gano masu su da kuma inda za su kai kayan abincin.

Chafe ya kara da cewa aikin ya zama dole, lura da yanayin hauhawar farashin kayayyakin abinci a kasar.