Kwastam ta kama motoci da shinkafar Naira miliyan 22 a Kaduna
Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, Kwastam cibiyar Zone `B’ ta kama motoci 4 dauke da buhun-hunan shinkafa 720 da aka yi fasa kwaurinsu da kudinsu ya kai sama da Naira miliyan 22. Kwatirolan shiyyar Mohammed Sarkin Kebbi ne ya sanarwa manema labarai hakan a Kaduna a karshen mako ya kuma ce, buhu guda 650 […]
Shinkafar da Kwastam suka kama.jpg1
Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, Kwastam cibiyar Zone `B’ ta kama motoci 4 dauke da buhun-hunan shinkafa 720 da aka yi fasa kwaurinsu da kudinsu ya kai sama da Naira miliyan 22.
Kwatirolan shiyyar Mohammed Sarkin Kebbi ne ya sanarwa manema labarai hakan a Kaduna a karshen mako ya kuma ce, buhu guda 650 na shinkafar an rufe su ne da albasa a cikin motar tirelar da aka kama a hanyar Sakkwato zuwa Gusau jihar Zamfara.
Sauran kananan motocin kirar Volkswagen Golf da aka kama a cikin makon nan sun dauko buhunan shinkafa 80 a ciki.