Kwastam ta kama shinkafar fasakwauri da aka voye a coci

A daidai lokacin da Hukumar Kwastam ke zage dantse don dakile ayyukan ’yan fasakwauri, a vangaren masu fasakwaurin suna kara fito da sababbin hanyoyi da dabarun fasakwaurin shinkafa zuwa kasar nan. A ranar Litinin da ta gabata jami’an Kwastam da ke aiki da ofishin hukumar a Abeokuta, Jihar Ogun sun gano tarin shinkafar da aka yiwo […]

Kwastam ta kama shinkafar fasakwauri da aka voye a coci

A daidai lokacin da Hukumar Kwastam ke zage dantse don dakile ayyukan ’yan fasakwauri, a vangaren masu fasakwaurin suna kara fito da sababbin hanyoyi da dabarun fasakwaurin shinkafa zuwa kasar nan. A ranar Litinin da ta gabata jami’an Kwastam da ke aiki da ofishin hukumar a Abeokuta, Jihar Ogun sun gano tarin shinkafar da aka yiwo fasakwaurinta da aka voye a wani coci a yankin Owode Yewa da ke daura da kan iyakar Najeriya Jamhuriyyar Benin ta yankin Idiroko.

Kakakin Hukumar Kwastam a Jihar Ogun, Abdullahi Maiwada, ya shaida wa Aminiya cewa motoci 40 makare da shinkafar fasakwauri hukumar ta kama a cikin cocin, inda ya ce, baya ga cocin da ’yan fasakwaurin ke amfani da shi wajen voye shinkafar suna amfani da gidajen jama’a a yankin da sauran wurare don voye shinkafar. Ya ce jami’an Kwastam din sun gamu da tirjiya daga masu fasakwauri kafin su kwace shinkafar. “Idan ba ka manta ba a irin haka ne a makonni biyu da suka shude masu fasakwaurin suka hallaka mana jami’inmu daya suka kuma raunata daya. A wannan karo ma  masu fasakwaurin da wadansu vatagari mazauna yankin sun rufar wa jami’anmu lokacin da suka je kwashe shinkafar har sai da jami’anmu suka yi harbi a sama domin su kare kansu gudun kada a maimaita abin da ya auku na kisan jami’inmu da aka yi  mako biyu da suka shude, da kyar jama’ar yankin suka bar jami’anmu suka yi aikinsu,” inji shi.

Ya ce, tilas jami’ansu suka janye domin wanzuwar zaman lafiya bayan da masu fasakwaurin suka bude masu wuta inda jami’an nasu suka mayar da martani domin kare kansu, “Gungun masu fasakwaurin sun rufe babbar hanyar Idiroko suna hayaniya suna  farautar  jami’an Kwastam domin su kashe, sun yi kokarin fito-na-fito da jami’an tsaron da suka shiga tsakani inda suka so su, ketare su su farwa jami’anmu a ofisoshinmu da ke yankin,” inji shi.

Maiwada ya ce, aikin da jami’ansu ke yi na hana fasakwauri suna yi ne domin inganta tattalin arzikin kasa kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta umarce su. Ya ce ba za su saurara ba wajen cika umarnin gwamnati tare da yin aikinsu yadda ya kamata. “Don haka muna godiya ga al’ummar yankin da ke ba mu goyon baya wajen gudanar da ayyukanmu da ma sauran jami’an tsaro da ke dafa mana a ayyukan da muke yi na kawar da ayyukan masu yi wa tattalin arzikin zagon kasa,’ inji shi.

Wata majiya ta ce masu fasakwaurin sun rufe hanyar Idiroko ne, suna zargin jami’an Kwastam da hallaka musu mutum guda a lokacin musayar wutar da suka yi.