Kwastam ta kama taramadol na Naira biliyan 12 a Legas
A makon jiya ne hukumomin Kwastam na Apapa da Tin-Can da Seme a Jihar Legas suka bayar da sanarwar kama kwayoyin Taramadol da rubabbun buhunan shinkafa na fiye da Naira biliyan 12 da kuma jiragen sama masu saukar ungulu biyu, bayan da jami’an na kwastam suka ki karbar Naira miliyan 150 a matsayin na-goro don su […]
A makon jiya ne hukumomin Kwastam na Apapa da Tin-Can da Seme a Jihar Legas suka bayar da sanarwar kama kwayoyin Taramadol da rubabbun buhunan shinkafa na fiye da Naira biliyan 12 da kuma jiragen sama masu saukar ungulu biyu, bayan da jami’an na kwastam suka ki karbar Naira miliyan 150 a matsayin na-goro don su bar kayan su wuce.
A bangare daya kuma an kama wadansu jami’ai da ake zargin suna da hannu wajen barin kayan su wuce daga wurin da suke bincike.
A ranar Alhamis din makon jiya ne Shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa, Kanar Hameed Ali ya baje kolin wasu sundukai 40 dauke da kwayoyin Taramadol da aka haramta shigo da su cikin kasar nan da jiragen sama masu saukar ungulu biyu a cikin sundukan da aka kiyasta kudin kayan a kan Naira biliyan 7 da miliyan 138.
Ya ce an yi dabarar lullube kayan ne da buhuna 388 domin bad-da-kama. Da yake nuna kayan ga manema labarai a harabar ofishin Kwastam da ke gabar teku na Apapa, Kanar Hameed Ali ya ce, bincike ya tabbatar da cewa an shigo da kwayoyin ne daga kasar Indiya a yayin da aka shigo da jiragen biyu daga Amurka. Ya ce, bincike ya nuna cewa ana so a yi amfani da jiragen ne wajen aikata miyagun ayyuka a kasar nan.
“Wani abin farin ciki shi ne irin yadda wadansu jami’an Kwastam masu alhakin tsare wadannan sundukai suka nuna kishin kasa, wajen kin karbar Naira miliyan 150 da aka mika musu a matsayin na-goro domin su saki sunduki daya tal daga cikin sundukai 40 da aka kama,” inji Hameed Ali
Haka ya ce an kama mutum uku har da wadansu jami’an Kwastam da suka yi ha’inci wajen tantance kayan kafin su isa wurin da aka kama su. Da zarar an kammala bincike za a gurfanar da mutanen a gaban kotu domin yanke musu hukumcin da ya dace da laifin da ake zargin sun aikata.
Bugu da kari a makon jiya Mataimakin Kwanturola Janar, Austin Chidi ya wakilci Kwanturola Janar Hameed Ali wajen nuna wasu sundukai 13 masu dauke da kwayoyin Taramadol da wasu miyagun kwayoyi daban da magungunan shafawa domin sauya fatar jikin dan Adam na fiye da Naira biliyan 3 da miliyan 134. Su ma wadannan kaya an shigo da su ne daga kasar Indiya inji shi.
Wakilinmu ya gana da Kwamandan Hukumar ta Tin-Can, Kwanturola MB Musa wanda ya nuna bakin cikin kan yadda wadansu hamshakan masu kudi suke amfani da dukiyarsu wajen yin odar miyagun kwayoyi da suke lalata kwakwalwar miliyoyin jama’a maza da mata, maimakon yin amfani da dukiyar tasu wajen gina kasa.
Da yake amsa wata tambayar, Kwanturola Musa ya ce, “Yanzu an canja na’urar binciken kwakwaf da muke aiki da ita a baya. Yanzu sabuwar na’ura mai gani har hanji da muka samu tana ba mu damar gano komai a cikin sunduki tun kafin mai karbar kaya ya kawo mana takardun da ke dauke da bayanan irin kayan da suka rubuta a ciki. Da zarar sun kawo mana takardu masu dauke da bayanan karya na kayan da suka yi oda nan take sai mu yi awon gaba da su domin tun kafin isowarsu mun riga mun gano irin kayan da ke cikin sundukan da suka zo karba.”
Shi ma Kwamandan Hukumar na iyakar Seme, Kwanturola Muhammed Uba Garba ya nuna wa manema labarai katan 57 na kwayoyin Taramadol da buhunan shinkafa dubu 16 da 729 da motocin alfarma 21 da buhunan sukari 378 da jarkoki 128 na man fetur da man gyada da diloli 40 na kayan gwanjo da sauran kayan bukatun yau da kullum da aka kiyasta kudinsu kan fiye da Naira biliyan 2 da miliyan 839.