Kwastam ta lalata maganin kara karfin sha’awa a Sakkwato
Hukumar Kwatsam ta Najeriya ta lalata maganunan kara karfin saduwa aure a Jihar Sakkwato.
Hukumar Kwatsam ta Najeriya ta lalata maganunan kara karfin sha’awa a Jihar Sakkwato.
Magungunan kara karfin sha’awa da hukumar ta lalata na daga cikin jerin jabun magunguna da wadanda amfaninsu ya kare da ta kama a shekarar 2023.
Kwanturolan Kwastam mai kula da shiyyar Sakkwato, Musa Omale, ya ce, “maganin kara karfin sha’awa da wasu magunguna marasa rajista na daga cikin kayan da muka lalata.”
Sauran sun hada da kayan abinci da madara da dai sauransu da aka kwace a sassan jihar.
Kwanturolan ya ce ana ci gaba da bincike domin gurfanar da wadanda suka yi fasakwaurin kayan domin a gurfanar da su a kotu.
Daga nan ya gargadi masu fasakwaurin da su daina muguwar sana’ar ko su gamu da fushin hukuma.