Kwastam ta samu biliyan 15 a Jihohin Osun da Oyo a bara
Hukumar hana Fasa kwauri ta kasa wato Kwastom shiyyar jijojin Osun da Oyo ta bayyana samun harajin da ya kai Naira biliyan 15 tsakanin watan Janairu zuwa Disamban bara. Shugaban shiyyar Mista Richard Oteri ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya sanya wa hannu, a garin Ibadan. Ya kara da cewa an samu […]
Hukumar hana Fasa kwauri ta kasa wato Kwastom shiyyar jijojin Osun da Oyo ta bayyana samun harajin da ya kai Naira biliyan 15 tsakanin watan Janairu zuwa Disamban bara.
Shugaban shiyyar Mista Richard Oteri ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya sanya wa hannu, a garin Ibadan. Ya kara da cewa an samu kudin hajarin ne daga tsofaffin motocin da ake shigo da su kasar nan. Wannan na nufin an samu karin kashi 10 cikin 100 daga harajin da aka samu a shekarar 2013, inda aka samu Naira biliyan 12.
Mista Oteri ya kuma yi karin haske game da yawan motocin da aka kwace a shiyyar, inda ya ce hukumar ta karbe motocin guda 453 lokacin da aka yi yunkurin fasa kwaurin shigo da su kasar nan. Hakazalika, ya ce sun kwace albarusai dubu 30 wadanda aka boye a cikin doya da kuma garin rogo, sai buhuhunan shinkafa guda dubu 14 da 636 da kuma sauran kananan buhuhunan shinkafa. Har ila yau, jami’in ya ce an kwace buhun hodar ibilis guda125 da kuma sauran kananan kayayyaki.