Kwastam ta yi kame a Legas
Rundunonin hadin guiwa na soja da jami’an kwastam sun kama buhunan shinkafa fiye da dubu 6 da dari 5 da aka kiyasta darajar kudinsu a kan fiye da Naira miliyan 1 da dubu 20, da aka yi fasa-kwaurinsu aka boye a cikin wadansu gidaje a kauyukan Ere a Jihar Ogun da Gbaji a Jihar Legas. […]
Rundunonin hadin guiwa na soja da jami’an kwastam sun kama buhunan shinkafa fiye da dubu 6 da dari 5 da aka kiyasta darajar kudinsu a kan fiye da Naira miliyan 1 da dubu 20, da aka yi fasa-kwaurinsu aka boye a cikin wadansu gidaje a kauyukan Ere a Jihar Ogun da Gbaji a Jihar Legas. Kamen ya biyo bayan samamen da rundunonin suka kai wadannan kauyukan ne a lokuta daban -daban.
Da yake zantawa da ’yan jarida tare da nuna masu buhunan shinkafa dubu 2 da dari 3 da rundunar ta kama a samamen na ranar Alhamis ta makonjiya, Kwamandan Rundunar Kwastam ta Seme Kwanturola Muhammed Aliyu, ya ce, dokar da ta kafa hukumar kwastam ta kasa ita ce ta tanadi ikon kai samame da yin wannan kamen a cikin gidaje da tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama da makamantansu.
Kwanturola Aliyu ya ce, wannan doka ce ta ba su damar yin dirar mikiya ga al’ummomin kauyen Gbaji, a inda suka yi kamen a gaban Hakimin kauyen da mukarrabansa, wadanda suka nuna goyon baya ga daukar wannan mataki na dakile ayyukan fasa-kwauri da ake fakewa da kauyensu wajen yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya.
Ya jinjina wa Kwamandan bataliyar soja da ke Badagry, Kanar U B Garba, wanda yake taimaka wa wajen bayar da hadin kai ga rundunar kwastam ta Seme.
A daidai wannan lokacin ne Kwanturola Muhammed Aliyu ya nuna wa ’yan jarida wata babbar motar kwasar shara da aka cunkusa tayoyin mota a ciki domin yin bad-da-kama da nufin shigowa da su cikin kasa ta haramtacciyar hanya. Haka kuma ya nuna wata karamar motar alfarma da aka manna hoton wani mamaci a jikin kofofi da gilashin motar da aka ce gawar mamacin ce a ciki da nufin shigowa da motar ba tare da biya mata harajin fito ba, amma asirinsu ya tonu aka kama motar.
Shi kuwa Kwanturola Muhammed Uba Garba na FOU Ikeja, cewa ya yi, rundunar ta yi kamen abubuwa daban-daban sau 128 a cikin watan Satumba. An kiyastakimar kudin kayan a kan fiye da Naira miliyan 356, daga cikin kayan da aka kama da sun hada da buhunan shinkafa dubu 4 da dari 2 da aka gano a cikin wadansu gidaje 3 a kauyen Ere. Sauran kayan sun hada da kananan motocin alfarma da suturun gwanjo da daskararrun kaji da sudaddun tayoyin mota da kudi da miyagun kwayoyi da tabar wiwi, inda rundunar ta mika wadansu kayan ga hukumomin NAFDAC da NDLEA da SON domin tantance ingancinsu.