Kwastam za ta raba wa jama’a kayan abincin da ta kwace
Hukumar Kwastam za ta raba wa ’yan Najeriya kayan abinci da ta kwace domin rage musu wahalhalun da suke ciki a halin yanzu.
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana shirinta na raba kayan abinci da ta kama ga ’yan kasar domin rage wahalhalun da suke fuskanta a halin yanzu.
Hukumar ta ce za a yi rabo kayan abincin ne bayan an tantance su an tabbatar da cewa ba su da hadari ga lafiyar dan Adam.
Dubban ’yan Najeriya dai sun gudanar da zanga-zanga a kan tituna kan halin kunci da tsadar kayan masarufi a kasar.
A kan haka ne ranar Talata shugaban hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana shirinsu ba raba kayan abincin da aka kama ga ’yan Najeriya.
- Mai Kula da Dakin Kabarin Manzon Allah ya rasu
- Ya kamata Hukumar Kwastam ta sakar wa ’yan kasuwa mara — Sarkin Kano
Kakakin Hukumar Kwastam, Abdullahi Maiwada, ya sanar cewa daukar matakin ya dace da aniyar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na watsa kasa a abinci.
A cewarsa, matakin na gaggawa ne kuma daukar sa na da muhimmanci wajen samun wadatar abinci a Najeriya da kuma dakile illar karancinsa ga ’yan kasa.
“Za a sanar da hanyoyin da za a bi wajen rabon kayan ta ofishin hukumar a duk fadin Najeriya, domin tabbatar da adalci da kuma yin koma a don tabbatar da cewa amfanin ya isa ga wadanda suka fi bukata,” in ji shi.