Kwastoma ya sace kudin da ya biya karuwa

Bayan sun kammala sai matashin mai shekaru 28 ya sace N3,000 da ya biya ta da kuma wayarta

Kwastoma ya sace kudin da ya biya karuwa

Zama Kotu. (Hoto: Aminiya)

An gurfanar da wani matashi a gaban kotu bisa zargin sace kudin da ya biya wata mace mai zaman kanta da ya yi lalata da ita.

Dan sanda mai gabatar da kara, Salewa Ahmed, ya shaida wa kotun da ke zamanta a Ibadan, Jihar Oyo, cewa matar ce ta kai kara cewa matashin mai shekaru 28 ya sace N3,000 da ya biya ta da kuma wayarta.

Salewa Ahmed, ya sanar da kotun da ke zamanta a Ibadan, jihar Oyo, cewa wanda ake zargin an kama shi ne bayan matar ta kai rahoto a caji ofis na Idi-Aro cewa kwastoman nata ya damfare ta.

Dan sandan ya shaida wa alkali cewa bayan sun gama lalata ne matashin ya biya ta kudin da suka amince a ranar 19 ga watan Janairu, amma ya faki idonta ya koma dakin ya sace kudin da kuma wayarta da kudinta ya kai N46,000.

Matashin dai ya musanta zargin da ake masa a gaban babbar kotun majistaren da ke yankin Mapo a garin Ibadan.

Daga nan alkalin kotun, Misis OO Latunji ta ba belinsa a kan kudi N100,000 bisa sharadin zai kawo amintattun mutane biyu da za su tsaya masa, kuma dole su kasance suna da dangantaka ta jini da shi.

Daga nan ta dage sauraron karar har zuwa ranar 26 ga watan Fabrairu. (NAN)

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume