Kyakkyawan kudiri ke haifar da kyakkyawar nasara
Duk abin da mutum zai yi matukar ya na da manufa ko kudiri mai kyau to da ikon Allah zai samu kyakkyawar nasara. A mafi yawan lokuta mutane ba sa gina al’amuransu a kan kudiri mai kyau, za ka samu sun boye wani abu cikin ransu, sabanin wanda za su nuna wa mutane a fili, […]
Duk abin da mutum zai yi matukar ya na da manufa ko kudiri mai kyau to da ikon Allah zai samu kyakkyawar nasara. A mafi yawan lokuta mutane ba sa gina al’amuransu a kan kudiri mai kyau, za ka samu sun boye wani abu cikin ransu, sabanin wanda za su nuna wa mutane a fili, matukar haka ta kasance to tabbas ba za ka taba ganin daidai ba, domin kuwa shi ramin karya kurarre ne, sannan an ce karya fure take ba ta ‘ya’ya. Tun da kake ba ka taba jin an ce ‘’Yau gaskiyar wane ta kare ba’’ sai dai ka ji an ce ‘’Yau karyar wane ta kare’’ To ashe samar da kudiri mai kyau a duk abin da za ka yi ya na da matukar amfani ga al’amuranka, idan ya zamto kana aikata abubuwa ba tare da kyakkyawan kudiri ba to ba za ka taba samun nasara ba, za ka kasance ne cikin farin ciki na dan kankanin lokaci.
Duk abin da za ka yi, ka yi shi don Allah da zuciya daya idan har kana son ka samu nasara, da zarar ka saka munafurci da yaudara to ka samar da hanyar da za ka rusa kanka da kanka, ba za ka taba ganin daidai ba.
Idan ka himmatu wajen cimma wani kudirinka ya na da kyau a ce ka nutsu sosai kada ka sanya yaudara, ko munafurci saboda da zarar mutane sun gane kai mayaudari ne to taka ta kare duk da cewa wasu mutanen sun dauke ka cewa idan ka na bukatar kai gaci a wani kudirinka cikin gaggawa sai ka hada da yaudara, wanda kuma hakan ba shi ne abu mafi dacewa ba. Bahaushe ma cewa ya yi ‘’Abin da ka shuka shi zaka girba.’’ Wannan karin magana ma ta nuna mana cewa idan ka gina lamarin ka da mummunar manufa to ba za ka taba ganin daidai ba.
Yan siyasa, masu kafa kungiyoyi da sunan taimako muna fatan za ku rika gina lamuranku a kan kyakkyawan kudiri, ma’ana tsakani da Allah.
Ya Allah Ka taimake mu akan lamuranmu, duk abin da za mu yi mu gina shi a kan kyakkyawan kudiri, wanda hakan ne zai kai mu ga cimma burinmu ko kuma samun kyakkyawar nasara. Naseer ya’aky
[email protected] 08100229688/09073801967.