Kyakkyawan misali daga El-Rufa’i
A ranar Litinin da ta gabata (23/9/19) ce Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya shigar da dansa mai suna Abubakar Sadik El-Rufa’i makarantar firamare ta gwamnati a matsayin wani bangare na yunkurin da gwamnatinsa ke yi wajen inganta makarantun gwamnati da nufin bunkasa harkar ilimi a Jihar Kaduna. Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce ya […]
A ranar Litinin da ta gabata (23/9/19) ce Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya shigar da dansa mai suna Abubakar Sadik El-Rufa’i makarantar firamare ta gwamnati a matsayin wani bangare na yunkurin da gwamnatinsa ke yi wajen inganta makarantun gwamnati da nufin bunkasa harkar ilimi a Jihar Kaduna.
Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce ya kai dansa makarantar gwamnati ce domin cika alkawarin da ya yi cewa idan dan nasa ya cika shekara shida zai sanya shi a makarantar gwamnati saboda a karfafa kokarin da ake yi na farfado da makarantun gwamnati.
Sai dai kuma mutane da dama sun dauka Mai girma Gwamna zai shigar da dan nasa makarantar firamare irin na sauran jama’a kamar wadda take Badikko kusa da Gidan Gwamnati ne, amma sai aka ga ya kai dan nasa makarantar gwamnati wadda ta fi kowace kyau da inganci, wato makarantar Kaduna ‘Capital School,’ wadda makaranta ce ta ’ya’yan manyan mutane.
Tun farkon kafa makarantar ‘Capital School’ ta Kaduna ’ya’yan Turawa da manyan ma’aikatan gwamnati da ’ya’yan masu hannu da shuni kawai ake dauka a makarantar, lokacin mulkin Balarabe Musa ne ya ce a bude wa kowa kofa ya shigar da ’ya’yansa.
Duk da haka Gwamna El-Rufa’i ya kyauta da ya kai dansa wannan makaranta, domin akwai makarantu masu zaman kansu da yawa a garin Kaduna da suka fi ta inganci, amma ya hakura ya bar dansa ya cakudu da sauran yara ’ya’yan talakawa wadanda suke zaune a aji mai cinkoso da dalibai uku ke zaune a kujera daya.
Hakan da ya yi zai sanya a mayar da hankali wajen gyara makarantar, kuma shugabannin makarantar za su mayar da hankali wajen tabbatar da cewa malamai suna aikinsu sosai domin Gwamna zai rika sanin halin da makarantar ke ciki a kowane lokaci.
Idan da sauran manyan ma’aikatan gwamnati za su amsa kiran da Mai girma Gwamna ya yi musu na cewa su daure su yi koyi da shi, da abin ya kara armashi, domin dole za a rika kulawa da makarantun, yadda za a tabbatar ana samun ilimi mai inganci a cikinsu.
Idan da hali ba shawara ya kamata Gwamna El-Rufa’i ya ba manyan ma’aikatan gwamnati ba, tilasta su ya dace ya yi, yadda duk wani jami’in gwamnati zai rika sanya ’ya’yansa a makarantun gwamnati, har zuwa babbar sakandare.
Abin takaici ne yadda a yanzu za ka ga hatta malamin makarantar gwamnati ba ya sanya dansa a makarantar da yake koyarwa, sai dai ya sanya shi a makaranta mai zaman kanta, saboda kowa ya yi imanin cewa an fi koyarwa a irin wadancan makarantu, alhali ba haka ba ne. Domin mafi yawan makarantu masu zaman kansu ba su da kwararrun malamai, inda suke da su kuma ba a biyansu da kyau, saboda haka ne malaman ba su mayar da hankali sosai, masu makarantun ne kawai suke cin moriyar makarantun ta hanyar tsawwala wa iyayen yara kudi amma su biya malamansu kudi kadan.
Idan aka inganta makarantun gwamnati mutane da yawa za su sanya ’ya’yansu, domin dole ce ta sanya wadansu ke kai ’ya’yansu makarantun kudi, domin ba su da kudin, matsa wa kansu kawai suke yi. Idan har aka yi sa’a gwamnati ta gyara makarantunta suka zama abin sha’awa, ma’aikata da sauran jama’a za su samu saukin rayuwa, domin a halin yanzu kudin makaranta na cikin abubuwan da suke takura wa mutane.
A kasar Rwanda gwamnati ta inganta makarantun gwamnati wanda ya sanya mutane suke ta cire ’ya’yansu daga makarantu masu zaman kansu suna mayar da su na gwamnati, domin kyawunsu da ingancinsu.
Wannan matakin ya sanya makarantu masu zaman kansu sun shiga cikin halin kaka-ni-ka-yi, wasu makarantun ma dole sai dai rufe su aka yi, domin babu dalibai, wadanda suka rage kuma suna fama da matsaloli, ba su iya biyan albashi, sai su kwashe watanni biyar ba su biya albashin wata guda ba. Har sai da ta kai masu makarantun sun koma suna rokon gwamnati ta taimaka musu.
Sai dai kuma a Najeriya da yake akwai jami’an gwamnati da suke da jari a wasu makarantu masu zaman kansu ban sani ba ko za su bari a farfado da makarantun gwamnati, kamar yadda aka yi a kasar Rwanda.
Lallai babu shakka matukar ’ya’yan jami’an gwamnati suna zuwa makarantu masu zaman kansu babu yadda za a iya inganta makarantun gwamnati, domin su ne za su kula da makarantun, tunda babu ’ya’yansu a ciki ba za damu da halin da suke ciki ba, sai malaman makarantun gwamnati su yi ta yajin aiki ba a damu da su ba, domin wadanda za su share musu hawaye wannan yajin aikin bai shafi karatun ’ya’yansu ba.
Allah Ya sa sauran gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati su yi koyi da El-Rufa’i, ta hanyar sanya ’ya’yansu a makarantun gwamnati su yi karatu tare da ’ya’yan talakawa, ba kuma su bude makarantar gwamnati da za a ingantata domin ’ya’yansu kawai ba.