‘Kyakkyawar dangantaka tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa zai kawo ci gaba’
Shugaban Majalisar Dokoki ta karamar Hukumar Dawakin Tofa Alhaji Abdulmumini Yakubu Sarauniya ya ce samun kyakkyawar dangantaka a tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa shi ne ginshikin samar da ingantaccen ci gaba a tsari mulkin dimokuradiyya.Alhaji Abdulmumini Yakubu Sarauniya ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya, inda ya cewa idan akwai kyakkyawar fahimtar juna […]
Shugaban Majalisar Dokoki ta karamar Hukumar Dawakin Tofa Alhaji Abdulmumini Yakubu Sarauniya ya ce samun kyakkyawar dangantaka a tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa shi ne ginshikin samar da ingantaccen ci gaba a tsari mulkin dimokuradiyya.
Alhaji Abdulmumini Yakubu Sarauniya ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya, inda ya cewa idan akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakanin majalisun dokoki da bangaren zartarwa za a samu ci gaba a kowane mataki na gwamnati.
Ya ce ’yan majalisar dokoki na kasar nan suna kokari wajen tabbatar da ganin an samu hadin kai da dangantaka mai kyau a tsakaninsu da bangaren mulki a matakan kasa da jihohi da kananan hukumomi 774 da ake da su, kuma haka ya sanya ake gudanar da mulki cikin nasara.
Alhaji Abdulmumini Sarauniya ya ce da yardar Allah Najeriya za ta zamo kasa abar misali ganin Shugaban kasa Muhammadu Buhari jagora ne tsayayye wanda yake da niyyar kawo ingantaccen sauyi a kasa tare da dora al’umma a kan sahihiyar hanyar rayuwa mai inganci duk da irin kalubalen da ke gaban gwamnatinsa na barnar da aka dade ana yi a baya.