Kyamar darussan harsunan gida a makarantu, laifin wane ne?
Hakika an dade ana ganin laifin dalibai da iyayensu dangane da kin darussan harsunan gida da daliban ke yi, wadansu na ganin iyayen ne da laifi wadansu kuwa na ganin laifin na dalibai ne. Abin mamaki kuma cikin masu yin wannan maganganu har da malaman jami’a bayan kuma su sun san ba laifin dalibai ko […]
Hakika an dade ana ganin laifin dalibai da iyayensu dangane da kin darussan harsunan gida da daliban ke yi, wadansu na ganin iyayen ne da laifi wadansu kuwa na ganin laifin na dalibai ne. Abin mamaki kuma cikin masu yin wannan maganganu har da malaman jami’a bayan kuma su sun san ba laifin dalibai ko iyayensu ba ne. Ko da yake dama Hausawa sun ce laifi tudu ne mutum nasa yake takawa ya hango na wani.
Sai dai ni tun daga lokacin da aka fara wannan maganar ta jingina wannan laifi ga dalibai da iyayensu ban taba amincewa da hakan ba domin kuwa kulba ce ke barna amma ake cewa jaba ce. Ina ganin kuma jingina musu wannan laifi ba karamin rashin adalci ne ba domin kuwa ga masu laifi nan karara indai har gaskiya za a fada.
Kin darussan harsunan gida a wurin dalibai ni a nawa ganin ba laifinsu ne ko na iyayensu ba, laifin gwamnatoci ne musamman na Tarayya da Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Kula da Jami’o’i (NUC) da kuma Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu (JAMB) amma fa sai mai son gaskiya ne kuma idan ya yi nazari zai yarda da haka.
Dalilin da ya sa na ce gwamnati tana da laifi a cikin wannan matsala shi ne kowa ya san gwamnati ita ce uwar al’umma don haka tilas ta zama komai da ruwanka musamman a irin wannan fanni mai matukar muhimmanci amma ina, sai ta janye hannunta ta zama ba ruwanta da yaya yanayin koyarwa yake tafiya a makarantu. Daga an yi kasafin shekara ta cire wa ilimi dan abin da ya samu shi ke nan kuma ba ta kara waiwaiyar fannin sai shekara ta juyo in za a yi wani kasafin. Haka duk lokacin da ta tashi daukar ma’aikatan tarayya musamman na tsaro sai dai ka ji an ce sai mai darasin Ingilishi da Lissafi (English & Mathematics) za a dauka maimakon a ce darasin harshen gida da lissafi misali; Hausa/Maths, Yoruba/Maths, Igbo/Maths amma ina ba ka taba jin haka ba. To ina ga in za a yi adalci iya wannan dalilin ma ya isa ya sa dalibai da iyayensu su fi karkata kan wadancan darussan fiye da na harshen gida tunda sun san ko sun same shi a banza in dai ba Ingilishi suka samu ba.
Kai bari in yi misali da jihata ta Jigawa, karo biyu gwamnatin jihar (ta yanzu) na dibar malaman makaranta masu shaidar kammala NCE ko jami’a amma ba a daukar masu fannin harshen gida iya darussan kimiyya, fasaha da kuma Ingilshi kawai ake dauka amma wanda ya yi wani karatun da ba su ba, to zaman banza ya yi a makaranta.
Ga shi a karo na uku ma abin da ta ce ke nan, ashe kuwa in dai har haka yake faruwa babu wani dalibi ko iyayensa da za su so ya bata wa kansa lokaci a kan wani darasi na harshen gida. Kai ba ma iya darasin harshen gida ba, darasin addini ma (IRK da CRK) an daina koyar da su a wasu ajujuwan makarantun kuma gwamnati da hukumar ilimi ne suka fito da wannan tsari, amma duk da haka wai ba a ganin laifin gwamnati sai na dalibai da iyayensu. Himm Allah dai Ya ba mu damar gyarawa!
Haka idan gurbin karatu dalibi yake nema a jami’a ba zai taba samu ba matukar ba darasin Ingilishi a takardarsa ta kammala sakandare koda kuwa ya fi kowa cin darasin harshen gida da ya karanta a aji, kun ga wannan ai laifin Hukumar NUC ce. Uwa uba kuma ga rawar da Hukumar JAMB ke takawa yayin rubuta jarrabawar sai a ce lallai sai dalibi ya yi jarrabawa a kan darasin Ingishi (use of English) koda kuwa ba Turancin zai karanta ba a jami’a, ita kuma ma’aikatar ilimi ta yi shiru kamar ba ruwanta ta kyale su sai cin karensu suke yi ba babbaka. Maimakon ta maida harkar koyarwar gaba daya ta koma da harshen gida kamar yadda kasashen da suka ci gaba suke yi amma ta ki ta kuma manta da cewa kayan aro ba ya rufe katara don kuwa babu wata kasa da ta ci gaba alhalin tana koyarwa da harshen aro.
Ina ganin wadannan dalilan da na lissafo a sama sun isa su zama hujja a gane cewa wannan laifin da ake cewa na dalibai da iyayensu ne, to, ba fa nasu ba ne na wadancan hukumomin ne. Kuma ya kamata mahukuntan kasar nan su sani babu yadda za a yi mu ci gaban da ake nema musamman a fannin ilimi matukar ba a dawo koyarwa da harsunan gida ba. Koda yake su ’ya’yansu ba a nan gida suke yin karatu ba. Sannan ya kamata su dauki misali daga kasar Indiya tana ci gaba ne sakamakon koyarwa da harshensu da suke yi haka kasar China da harshensu na Sinanci suke koyarwa dauki kasar Turkiyya da harshensu suke koyarwa hada da Japan, Iran, Rasha da Holland duk za ka ga da harsunansu na gida suke koyar da duk wani darasi kai ko nan Misar da harshensu suke koyarwa balle kuma Ingila ko Amurka. Amma mu ina? saboda mahukuntanmu ba burinsu gina kasa ba burinsu kawai idan sun samu mukamai su saci abin da jikokinsu na uku ma ba za su yi talauci ba.
Allah Ka shige mana gaba Ka kawo mana dauki a harkar koyo da koyarwa a Najeriya.
Daga K. Bello Kiyawa
(070-3252-8895)