Kyamar sana’a ta haifar da zaman banzan matasa

Hausawa mun taso rayuwarmu cikin tsari mai kyau, ba mu yarda da zaman banza ba. Zamani ya sa mun watsar da sana’o’inmu da muka gada iyaye da kakanni, wadanda tun kafin zuwan Turawa muna yinsu. Kowane gida za ka samu akwai abin da suka yi fice.  Wasu daga cikin abubuwan da Hausawa muka rika a […]

Kyamar sana’a ta haifar da zaman banzan matasa

Hausawa mun taso rayuwarmu cikin tsari mai kyau, ba mu yarda da zaman banza ba. Zamani ya sa mun watsar da sana’o’inmu da muka gada iyaye da kakanni, wadanda tun kafin zuwan Turawa muna yinsu. Kowane gida za ka samu akwai abin da suka yi fice.  Wasu daga cikin abubuwan da Hausawa muka rika a matsayin dogaro da kai sun hada da noma da saka da kira da jima da dukanci da sauransu. Kai ko a tsarin Unguwanni da muke da su zai nuna ma Bahaushe ada ya dogara da kansa, sabanin yanzu da muka zama cima zaune, muna jiran mu samu aikin gwamnati. Idan ka je tsohon gari dole ne ma ka samu irin wadannan unguwanni kamar haka: Majema da masaka da makera  da makamantansu. Idan ka je unguwar Masaka za ka iske Iyayen da ‘ya’yansu duk suna sana’ar saka, haka makera da sauransu. Yanzu an wayi gari mun watsar da sana’o’inmu. 

A wasu unguwannin ma idan ka je suna suka tara ba a sana’a mai sunan unguwar. Idan kuma ana yi ma ba za ka ga matasa ba sai dattijai ko kuma tsofaffin mutane. Matasa muna kyamar sana’ar da muka gada a gidanmu ta iyaye da kakanni. Matashi na kyamar a ga ya tafi gona, matashi na kyamar a ga ya na jima, matashi na kyamar a ga ya na kira, matashi na kyamar a ga ya na saka, Kai abubuwan da yawa. Laifin iyaye ne da kuma gwamnati ya sa matasa ke kyamar sana’ar iyayen nasu, saboda mafi yawa ba sa koyar da ‘ya’yan sana’ar ta su. 

Ita kuma gwamnati ta ki ta maida sana’o’in nazamani ta hanyar samar injinan da za su yi aiyukan a saukake kuma masu inganci. Lallai mu lalubo mafita. 

Hausawa Mu koyar da ‘ya’yanmu sana’o’in da muka gada iyaye da kakanni. Gwamnati ita kuma ta bada duk wata kulawa da ake bukata. Duk sana’ar da kake ka rika tafiya da danka wajen sana’ar tun ya na karami, ko ya girma ba zai kyamaci sana’ar ba.  Misali Tela ne kai, kafinta ne, manomi ne kai, ko ma mene ne kake ka koyar da ‘ya’yanka suna kanana, haka ba zai sa su kyamaci sana’ar ba ko da sun girma. Kun ga ashe da kowa ya girma da neman na kansa, yadda ko da mun yi karatun boko in ba mu samu aiki ba, ba za mu takura ba. 

Amma kacokam mun dogara da aikin gwamnati, wanda kamata ya yi ko kana aikin gwamnati ya zamto ka na dan taba wata sana’ar a gefe. A kalla kamata ya yi kowane matashi a ce ya iya sana’a kala biyu yadda duk inda rayuwa ta juya ba zai jigata ba. Akwai matsala a sa’ilin da tarin matasa suka kasance masu zaman banza a kasa, hadarin da za su zamewa kasa shine tamkar mai wasa da maciji ko mai wasa da wuka akan ruwan cikinsa. Allah ya sa mu dace. 

Nasiru Kainuwa Hadejia<[email protected]>08100229688/09073801967.