kyamar yara masu raunin hankali bai dace ba – Misis Katagum

Shugabar makarantar Zamarr Institute da ke lura da yara masu matsalar raunin hankali, Misis Khadeeja Oluronke Katagum, ta ce kyamar da mutane suke nuna wa yara masu matsalar raunin hankali ita ce babbar matsalar da yaran suke fuskanta.Misis Khadeeja Katagum ta bayyana haka ne lokacin da take tattaunawa da Aminiya a harabar makarantar da ke […]

kyamar yara masu raunin hankali bai dace ba – Misis Katagum
kyamar yara masu raunin hankali bai dace ba – Misis Katagum

Shugabar makarantar Zamarr Institute da ke lura da yara masu matsalar raunin hankali, Misis Khadeeja Oluronke Katagum, ta ce kyamar da mutane suke nuna wa yara masu matsalar raunin hankali ita ce babbar matsalar da yaran suke fuskanta.
Misis Khadeeja Katagum ta bayyana haka ne lokacin da take tattaunawa da Aminiya a harabar makarantar da ke Unguwar Jabi a Abuja.
Ta ce “Mutane da yawa ba sa hakuri da yara masu raunin hankali kuma ba sa hakuri da iyayen da suka haife su. Iyayen ba laifi suka yi wa Allah ba Ya ba su ’ya’ya masu raunin hankali kuma ba roka suka yi ba. Maimakon mutane su rika jawo su a jika sai su rika nuna musu kyama suna kyarar su. Wannan babbar matsala ce ga yaran da kuma iyayensu.”
Ta ce ya kamata mutane su gane cewa yaran da suke da wannan matsala su ma mutane ne kuma iyayen da suka haife su su ma mutane ne kamar kowa.
Misis Khadeeja ta ce kamata ya yi mutane su rika janyo su jika suna nuna musu kauna da soyayya. A nuna wa yaran yarda da kansu da kuma karfafa musu gwiwa tare da yin hakuri da su.
“Idan mutane suka daina kyararsu suka nuna musu so da kauna da kuma yin hakuri da su, yaran za su ji dadi sosai,” inji ta.
Sai ta ce hanya daya tilo ta taimaka wa yaran ita ce a kai musu dauki cikin gaggawa a duk lokacin da aka lura suna dauke da matsalar raunin hankali. “Idan iyaye suka dauki matakin gaggawa yayin da suka fahimci dansu na fama da matsalar raunin hankali, to babu shakka za a cimma burin da ake so amma idan aka yi sakaci, to sai a ga abubuwa sun dagule wa yaro. Matsalar raunin hankali ba ta warkewa amma ana samun sauki a samu ci gaba,” inji ta.
Misis Katagum ta ce makarantar ta cimma nasarori da yawa da suka kunshi taimakon yara masu raunin hankali da iyayensu da bayar da shawara a gare su tare da tallafa musu ta hanyoyi da dama.
Ta koka kan yadda wasu iyaye ke jingina matsalar raunin hankali da aljanu. “A wurare da yawa da zarar yaro ya gamu da matsalar raunin hankali sai ka ji ana cewa aljanu ne suka shafe shi. alhalin ba haka ba ne. Saboda haka idan iyaye suka lura cewa dansu yana da matsalar sai su yi gaggawar kai shi wurin kwararru da za su kula da shi,” inji ta.