kyanda ta halaka yara 40 a Kaduna
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kaduna (PHCDA) Dokta Sufyan Babale ya ce akalla yara 40 ne cutar kyanda ta halaka a jihar.Dokta Sufyanu Babale ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan da kammala wani taro da masu ruwa da tsaki a kan yaki […]

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kaduna (PHCDA) Dokta Sufyan Babale ya ce akalla yara 40 ne cutar kyanda ta halaka a jihar.
Dokta Sufyanu Babale ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan da kammala wani taro da masu ruwa da tsaki a kan yaki da cutar poliyo da sauran cututtuka masu halaka yara a ranar Alhamis din makon jiya.
Ya ce cutar ta halaka yaran ne a karamar Hukumar Lere da ke a Arewacin jihar. “Wannan mace-macen yaran sun faru ne a karamar Hukumar Lere kuma akalla yara sama da 30 ne suka rasu. Na kuma ziyarci karamar hukumar domin gane wa idona abin da ke faruwa. Kuma an zagaya da ni makabarta inda aka nuna min sababbin kaburburan yaran. Muna da jerin sunayen wadanda suka rasu. Sannan an samu bayanin bullur cutar a kananan hukumomi 23 da ke a jihar. Amma a yanzu al’amura sun daidaita saboda matakan da gwamnati ta dauka a kan lokaci,” inji shi.
Dokta Babale ya kara da cewa cikin matakan da suka dauka sun hada da neman goyon bayan malamai da ’yan jarida domin su taimaka wajen kara wayar wa iyayen yara kai su rika kai ’ya’yansu asibiti domin yi masu allurar rigakafi.
Ya ce, ba a cika samun tirjiyar iyaye kan allurar rigakafin cutar kyanda ba, saboda sun san hadarin da ke tattare da haka.
A jawabin Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Ambasada Nuhu Bajoga kira ya yi da babbar murya ga iyaye kan su tashi tsaye wajen nema wa ’ya’yansu lafiya ta hanyar kai su inda ake allurar rigakafin cutar.
Ya ce ko shakka babu allurar ana yin ta ne domin jin dadin yaran da iyayensu. “Wannan allura domin ku iyaye da yara ake yi saboda amfaninku ne da na ’ya’yanku,” inji shi.
Ya bukaci malamai da masu sarautun gargajiya su taimaka domin a samu nasarar kawar da da cutar a jihar baki daya.