‘Kyanwa biyu da Biri’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Yaya hutu? Allah Ya taimaka amin. A yau na kawo muku labarin ‘kyanwa biyu da Biri’. Labarin ya yi nuni da a duk lokacin da mutum biyu suke fada, na ukunsu ne ke cin ribar fadan. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi. Akwai wasu Kyanwoyi biyu wadanda ba su […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Yaya hutu? Allah Ya taimaka amin. A yau na kawo muku labarin ‘kyanwa biyu da Biri’. Labarin ya yi nuni da a duk lokacin da mutum biyu suke fada, na ukunsu ne ke cin ribar fadan. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi.
Akwai wasu Kyanwoyi biyu wadanda ba su cika shiri da juna ba. Ga yunwa ta damesu sosai. Ganin dukansu biyu suna jin yunwa, hakan ya sanya suka yanke shawarar fita tare domin yawon neman abincin ci.
Suna cikin tafiya sai suka tsinci burodi. Sai suka shiga fada domin kowanne daga cikinsu yana son cinye burodin shi kadai.
Ashe duk abin da suke yi wani Biri na kallonsu daga saman wata bishiya, sai ya sauko ya same su ya ce su fada masa abin da ya sa suke fada.. Koda suka fada masa ga shi shi ma yunwar yake ji, sai ya yanke shawarar ya raba musu burodin gida biyu. Idan ya raba sai ya ga daya ai daya ya fi daya girma, sai ya gutsura da baki, haka ya yi ta yi har sai da ya cinye burodin duka, daga nan ya ruga a guje.
Daga nan kyanyowin suka shiga yin nadama a kan fadan da suka yi, ga shi sun yi biyu babu.
Tun daga ranar suka daina yin fada da juna. Da fatan Manyan Gobe sun dauki darasi a wannan labari.