Kyanwa ta rayu ba abinci tsawon mako uku

Wata kyanwa ta bai wa wadansu ma’aikatan kamfanin dakon kaya a jirgin sama mamaki bayan samunta a raye, duk da kulle ta da aka yi a cikin kwantainar kaya na tsawon mako uku ba tare da abinci ko ruwan sha ba. Hakan ya faru ne a farkon watan Janairu inda kamfanin dakon kayan na kasar […]

Kyanwa ta rayu ba abinci tsawon mako uku

Wata kyanwa ta bai wa wadansu ma’aikatan kamfanin dakon kaya a jirgin sama mamaki bayan samunta a raye, duk da kulle ta da aka yi a cikin kwantainar kaya na tsawon mako uku ba tare da abinci ko ruwan sha ba.

Hakan ya faru ne a farkon watan Janairu inda kamfanin dakon kayan na kasar Ukraine mai suna Star Shine Shipping Ltd ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa hakan wani bakon abu ne, ta yadda aka samu kyanwar mai nisan kwana.

A lokacin da aka bude kwantainar da aka dauko kaya a cikinta wadda aka yi tafiya da ita nisan kilomita dubu biyu daga kasar Ukraine zuwa kasar Isa’ila, tafiyar da ta dauke su sama da mako uku, kafin ma’aikatan kamfanin sun gano kyanwar a cikin kayan da suka dauko.

Bayan bude kyanwar a cikin kwantainar ta ji tsoro amma tana cikin yanayi mai kyau, duk da dogon zangon da aka yi da ita  ba tare da ta ci abinci ko ta sha ruwa ba.

An wallafa hotunanta a shafin Facebook na Star Shine Shipping Ltd inda aka gano boyayyiyar fasinja zaune a kan kwalayen da aka yi dakonsu a cikin kwantaina.

Ita dai kyanwar kafin ta ankara ta tsinci kanta a tashar ruwan kasar Isra’ila. Daya daga cikin hotunan da aka wallafa ya nuna yadda aka jibga kwalayen alawa na kasar Ukraine.

Kyanwar bayan ta fito ta ci ta koshi

Duk da yake wadansu na mamakin yadda kyanwar ta rayu na tsawon kwanaki ba tare da abinci ko ruwan sha ba, yayin da aka rufe kowace kafa ta kwantainar, sai dai ana zargin kila tana lasan zakin da ke jikin kwalayen alawar idan ta ji kishin ruwa a lokacin da jirgin ke tafiya.

Bayan jin kukan kyanwar da aka yi, sai ma’aikatan Kamfanin Star Shine Shipping suka fara binciken abin da ke fitar da wannan sauti daga cikin kwalayen da aka dauko.

Hakan ya sa aka gano kyanwar a makale cikin kwalayen da aka dauko daga tashar jiragen ruwa ta Odessa sannan aka kulle tare da kyanwar bisa rashin sani.

Wadansu na tambaya kan yadda kyanwar ta rayu na tsawon mako uku a kulle, wanda ba a bayar da amsar haka ba.

Muhimmi shi ne kyanwar tana cikin koshin lafiya tare da kulawar kamfanin dakon kayan, kamar yadda Daraktan Kamfanin, Aledander Binnik ya sanar.

A cewar Aledander Binnik: ”Wannan ba shi ne na farko da kamfanin ya dauko wata dabba da ta rayu ba abinci ba.

A shekarar 2016, an wallafa labarin wani kwikuyo da ya rayu tsawon kwana 25 a cikin kwantainar dakon kaya ba tare da cin abinci ko shan ruwa ba.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Tags