Kyanwa ta yi tafiyar kilomita 370 makale a karkashin mota

Wata kyanwa mai ido daya da aka sanya mata suna Lucy wacce take kan hanyar komawa gida ta makale a karkashin wata babbar mota kirar tirela inda aka yi tafiya da ita na tsawon kilomita 370 daga birnin Hull zuwa Bristol da ke Ingila. An gano Lucy mai shekara 12 a wata tashar da ake […]

Kyanwa ta yi tafiyar kilomita 370 makale a karkashin mota

Wata kyanwa mai ido daya da aka sanya mata suna Lucy wacce take kan hanyar komawa gida ta makale a karkashin wata babbar mota kirar tirela inda aka yi tafiya da ita na tsawon kilomita 370 daga birnin Hull zuwa Bristol da ke Ingila.

An gano Lucy mai shekara 12 a wata tashar da ake sauke kaya inda wadansu ma’aikata da ke aiki a wurin suka gano magen da ranta.

Direban babbar motar ya yi tunanin Lucy ta mutu tun a hanya sanadiyyar doguwar tafiyar da ya yi. Lucy tana makale ne a tsakanin gurbin tayar tirilar, daya daga cikin ma’aikatan Dan Cartwright ya ce, direban ya yi tunanin duk wani abu mai rai da zai makale a wannan doguwar tafiyar ba zai rayu ba.

“Mun yi zaton Lucy ta mutu sai muka fahimci Lucy na daga kai sama, hakan ya sa muka jawo hankalin jami’an kiwon lafiyar dabbobi na RSPCA,” inji shi. Jami’an RSPCA din kuma sun binciki lafiyar Lucy.

Wanda ya mallaki Lucy, Paul Smith ya ce bai ji dadin rashin ganin kyanwarsa ba na wasu kwanaki, sai daga bisani aka sanar da shi an gano inda take. Paul dai ya ce, mahaifiyarsa tana kiran magen Lucy ne, hakan ya sa aka yi wa magen lakabi da Lucy.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana