Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (6)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi’un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi’un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah Ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.
Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, mun yi tsokaci mai tsawo dangane da nuni kan kyauta cikin kyauta-yi tare da kawo misalai masu yawa da manuniya kan muhimmancin wannan dabi’a daga Hadisan Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya isa ga mai hankali da lura ya kama aiki. Allah Ya kara mana taimakonSa. Yau, in Allah Ya so, za mu kammala mukalar daga cewa:
Babu shakka shi Musulunci yana haska sadaka ne da kyauta cikin kyauta-yi a wani yanayi da yake haifar da gwaggwabar ladar da take mafi girma a bangarensa, kamar dai yadda aka fitar a wani Hadisi daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa, “Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ya Ma’aikin Allah, wace irin sadaka ce ta fi?” Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Wadda ka bayar a lokacin da kake lafiyayye, kana kankame da dukiya (wato kana tsumulmularta), kana tsoron talauci, kana sa ran zama attajiri! (ita ta fi). Kada ka yi jinkiri har sai ka kusa mutuwa ka rika cewa, “Wannan a kai wa wane da wane; waccan a kai wa wane da wane.” Alhali ta kai lokacin da ta zama dukiyar wane da wane!” Buhari da Muslim ne suka ruwaito Hadisin. Wato -Allah Shi ne Mafi sani-, manufa kada a bari dukiya ta kai matsayin ta magada, domin mai ita ya kai gargarar mutuwa.
Musulmi na gaskiya, mai kyauta, shi ne yake bayar da sadaka (ko kyauta) musamman ga wadanda suke da bukatarta. Yakan duba a cikin matalauta da mabukata wadanda suke wadatuwa wajen su roki wani abu daga wajen kowa, ta yadda mafi yawan mutane sai su yi zaton ba su ma da bukata. Yakan je wajen irin wadannan mutane, ya iske su har gida ya ba su abin da zai ishe su biyan bukatarsu ta yau, ta yadda za su kange mutuncinsu. Irin wadannan mutane kuwa su ne na farko da za a je a ba su taimako. Su ne kuwa wadanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce game da su, “(Ainihin) mabukaci (matalauci) ba shi ne wanda yake (roko kuma yana) karbar dan wani abu shi ke nan ya juya ya tafi ba, a’a, mabukaci shi ne wanda ba ya da shi, ba ya da abin biyan bukatar kansa, amma ya kame daga tambayar (rokon) mutane, saboda ya tsare mutuncinsa.” Buhari da Muslim ne suke fitar da wannan Hadisin.
Musulmi na gaskiya, mai kyauta, shi ne yake bayar da sadaka (ko kyauta) ga maraya. Ya dauki nauyinsa, har zuwa lokacin da ya kai matsayin ya nemi na kansa, kuma ba ya damuwa ko bambancewa tsakanin marayan da yake da dangantaka da shi da wanda ba danginsa ba. Yana yin wannan aikin alherin ne da tunanin samun abin da wanda ya dauki nauyin maraya yake samu, wanda yake matsayi mai girma da daraja da za a iya saida rai ma don a same shi. Wannan kuwa matsayi ne na kasancewa tare da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a Aljannah, kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito Hadisi daga Sahlu dan Sa’ad, (Allah Ya yarda da shi), cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Ni da wanda ya dauki nauyin maraya, za mu kasance kamar haka a Aljanna,” sai ya nuna dan yatsarsa (dan-ali) da na tsakiya, ya wara su.”
Musulmi na gaskiya mai kyauta cikin kyauta-yi, shi ne yake bayar da sadaka (ko kyauta), ga wadda ta rasa mijinta (bazawara) da kuma matalauci, saboda yana bin shiryarwar addininsa, yana neman yardar Ubangijinsa, yana kwadayin ladar da Allah Ya tanada wa masu irin wannan aikin alheri.
Shi irin wannan aiki na tallafa wa wadda ta rasa mijinta da matalauta yana da ladar da ta kai ta yin azumin nafila da tsayuwar dare da kuma jihadi saboda daukaka kalmar Allah. Wannan lamari kuwa ya biyo bayan abin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Duk wanda ya mayar da hankali wajen daukar nauyin zawarawa da matalauta, to kamar wanda yake jihadi ne wajen daukaka kalmar Allah.” Mai ruwaya ya ce, ina da tabbacin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Haka nan ya yi kamar wanda ya tsayu cikin dare yana Sallah ba gajiyawa da kuma wanda ya dinga azumi ba kakkautawa.” Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.
Wadannan fuskoki da aka zayyana tun farkon wannan mukala, su ne wuraren da Musulmi mai kyauta cikin kyauta-yi zai rika bayar da dukiyarsa domin kwadayin samun kwanciyar hankali da natsuwar zuciya da faraga da kuma lada daga Allah.
Wadannan duk halaye ne da za su kusantar da bawa ga Ubangijinsa. Sannan ko kusa kada masu dukiya su yi zaton za su samu komai a cikin abin da suke kashewa wajen sharholiyar bayar da ci da sha ga jama’a da watsa kudi don kawai su nuna su, su ne, ko kuma don samun biyan wata bukata ta zukatansu. Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi tir da duk wata ciyarwar da ake yi ba don Allah ba, inda ya ce, “Tir da walimar da mawadata kadai ake gayyata, alhali ana kore matalauta daga gare ta.” Buhari da Muslim suka fitar da Hadisin.
A karshe, ana kara jan hankalin Musulmi ya gane cewa mayar da hankali wajen taimakon matan da suka rasa mazajensu da matalauta da daukar nauyin marayu, ba kawai yana samar da gwaggwabar lada ba ne, a’a, har ma yana wanke zuciya; ya kara kyautata zamantakewa; ya tausasa zukata; ya sa a more gardin kyauta cikin kyauta-yi; ya karsasa yin ayyukan alheri cikin nishadi da annashuwa. Shi ya sa ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yakan zaburar da masu kuncin rai da zafin zuciya, su rika kyauta da ayyukan kyauta-yi, ta yadda zukatan nasu za su yi taushi su cika da rangwame.
Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ba da labarin cewa wani mutum ya kai kukan tsaurin zuciyarsa ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya ce masa, “Ka (rika) shafa kan maraya, kuma ka rika ciyar da matalauta.” Imam Ahmad ne ya fitar da Hadisin kuma mazajen Hadisin ingantattu ne.
Da wannan muka zo karshen wannan mukala ta kyauta cikin kyauta-yi, tare da fatan daidai din da ke ciki, Allah Ya ba mu ladarsa, kuskure kuma Allah Ya gafarta mana, amin!
Wassalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuh.