Kyautar Kwankwaso ta janyo tsige shugaban kasuwa a Legas
Ga dukkan alamu, kyautar Naira miliyan daya da dubu dari uku da sittin da Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba wa kungiyar kasuwar masaukin alhazai da ke harabar filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke yankin Ikeja a Jihar Legas ta janyo tsige shugaban kungiyar, Alhaji Abubakar UAC daga kan […]
Ga dukkan alamu, kyautar Naira miliyan daya da dubu dari uku da sittin da Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba wa kungiyar kasuwar masaukin alhazai da ke harabar filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke yankin Ikeja a Jihar Legas ta janyo tsige shugaban kungiyar, Alhaji Abubakar UAC daga kan mukaminsa.
kungiyar kasuwar da a takaice ake kira kasuwar Haji-kam da ta hada da masu canjin kudin kasashen waje da masu sayar da abinci da nama da kayan masarufi da masu wankin takalmi na zargin Abubakar UAC da almudahana da rashin adalci da kuma cin amanarta.
Tuni kungiyar ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki tsohon shugaban kungiyar tare da kafa shugabancin rikon kwarya karkashin jagorancin Alhaji Bala Jantil da mataimakinsa dankaduna.
daya daga cikin ’yan kungiyar mai suna Dauda Mainama ya zargi Alhaji UAC da zalunci da cin amana da rashin adalci. “Ai mai arziki ake ba ajiyar kudi ba wanda ba shi da kudi ba. Ina ganin UAC ya zalunce mu kuma ya ci amanar da muka ba shi. A yanzu haka ana neman miliyoyin Naira a wurinsa, duk da albashin da kungiya take biyansa na Naira dubu hamsin duk wata, tare da cire kaso goma na duk rikicin kudin da ya shiga tsakani. Na san ya musguna wa jama’a a kan kudin sati. Mafi yawan aikin da ka ga an yi a kasuwar, masu hannu da shuni na kasuwar ne ke yi da kudinsu, ba shi ne ya yi ba. Shi sai dai ya cinye kudin da muka tara masa, abin da ya dade yana yi a kasuwar. Kudin Kwankwaso ne suka tona asirinsa”. Inji shi.
Tsohon sakataren kungiyar kasuwar, Alhaji Auwalu Azare, wanda ke yin canji a kasuwar, ya bayyana lamarin da tsautsayi.
Ya ce, “A sanina da Abubakar UAC, lokacin da na yi aiki da shi, ban taba ganin alamun ya ci kudi ba, don ba shi yake ajiye kudin kungiyar ba, duk kudin da zai bayar sai dai ya tura wurin mataimakinsa. Ni ina ganin matsalar ta taso ne daga masu karbar kudin kungiya da ’yan kungiyar da ba sa biyan kudin kungiya da kuma shugabannin kungiyar da ba sa cizawa suna hurawa”.
Sabon shugaban kungiyar na riko, Alhaji Bala Jantil ya ce ba shi da wata matsala da Abubakar UAC, shi kuma mataimakinsa dankaduna cewa ya yi ba zai ce komai ba domin kwamitin bincike da kungiyar ta kafa na ci gaba da aikinsa.
Shi kuwa Alhaji Abubakar UAC musanta zargin ya yi da cewa, “karya ce! Ni da ma ban karbi albashina na watanni fiye da biyar ba? Duk abin da na yi na ci gaban kungiya da bunkasa ta a kasuwar ba a gani ba? So dai ake a ci mini mutunci. Ba a ga fadi-tashin nemo ragin fiye da Naira dubu dari bakwai na kudin haya da na yi da gyare-gyaren da muka yi a kasuwa da tsaftace
kasuwanci da ’yan kasuwar da abubuwa da daman a ci gaba da muka yi ba. Ni da na sadaukar da kaina da lokacina da kasuwancina a kan kungiya, ba a gani ba, sai don wasu suna so su ci mutuncina shi ne za a rika tambayar kudin da Kwankwaso ya bayar da Naira dubu talatin da na biya kudin makarantar yara. Ai, a gabansu na tambayi ma’aji dangane da kudin Kwankwaso ya ce kudin suna nan a ajiye.
Ma’ajin kungiyar, Alhaji Garba Lamba daya, ya tabbatar da cewa kudin da Kwankwaso ya bayar suna nan, sai dai akwai ragi da kari da suka rika samu.
Binciken Aminiya ya gano cewa lallai Gwamna Kwakwaso ya raba miliyoyin naira a kasuwanni da dama a Legas din.
Da aka tuntubi mai magana da yawun gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Halilu dantiye, sai ya amsa ta sakon waya cewa, “Ka nemi kwamishina na ciniki, Dokta Abubakar Nuhu damburam. Shi ne ya kula da lamarin”.