Kyautar shiga daka kai kuka na yi wa Shata ya yi mini waka – Nagwandu Mai Nama

“Yaro Nagwandu mai naman nan.” Alhaji Garba Nagwandu Mai Nama, tsohon mahauci ne, dan kasuwa wanda kuma daya ne daga cikin dimbin mutanen da marigayi Dokta Mamman Shata Katsina ya yi wa waka, wadda a cikinta yake cewa “Yaro Nagwandu mai naman nan.” Aminiya ta tattauna da shi kan al’amuran da suka shafi tarihin rayuwarsa […]

Kyautar shiga daka kai kuka na yi wa Shata ya yi mini waka – Nagwandu Mai Nama

“Yaro Nagwandu mai naman nan.”

Alhaji Garba Nagwandu Mai Nama, tsohon mahauci ne, dan kasuwa wanda kuma daya ne daga cikin dimbin mutanen da marigayi Dokta Mamman Shata Katsina ya yi wa waka, wadda a cikinta yake cewa “Yaro Nagwandu mai naman nan.” Aminiya ta tattauna da shi kan al’amuran da suka shafi tarihin rayuwarsa da yadda aka yi har Shata ya yi masa waka. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ko za ka bayyana mana tarihinka?
Alhaji Garba:  Assalamu alaikum. Sunana Alhaji Garba Nagwandu Mai Nama, wanda yake zaune a Tudun Wada Kaduna. An haife ni a shekarar 1940 a garin Sabuwa da ke Jihar Katsina. Mun dawo Kaduna  tare da mahaifina a lokacin da nake da kimanin shekara tara da haihuwa, inda muka ci gaba da sana’ar fawa a unguwar Kawo. A lokacin duka makarantun Turawan mishan da ke garin nan, mu ne muke samar musu da abinci da kuma nama. Manyan guraren da muka yi  aiki da su a wancan lokacin sun hada da makarantu kamar su: kueen Amina da Rimi College, Technical College da ke Malali da otel din Hamdala da na Durbar da gidan gwamnatin Jihar Kaduna, lokacin mulkin Kanar Lawal Jafaru Isa da sauran muhimman wurare da dama. Hakazalika, a kan idonmu aka gina Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna wato (Kaduna Polytechnic), inda ita ma muka kasance cikin sahun farko na mutanen da suka samar mata da abinci. Duk wannan ya faru ne lokacin da duniya take kwance, lokacin da gwamnati ce take bai wa dalibai abinci kyauta.
Aminiya:Me ya sa ake kiranka Nagwandu?
Wannan sunan ya fara ne daga ranar da aka haife ni. Saboda a lokacin kakana ya dawo daga garin Gwandu da ke cikin Jihar Kebbi ta yanzu. Ko da isowarsa gida, sai aka shaida masa cewa mahaifiyata ta sauka lafiya. Da bude bakinsa, sai ya ce me aka samu. Aka bayyana masa cewa namiji ne. Daga nan sai ya kada baki ya ce a’a, an dai samu Nagwandu. Shi ke nan sunan ya bi ni har girma.
Aminiya: Wane lokaci ne ka fara haduwa da Shata?
Na fara yin ido hudu da marigayi Dokta Mamman Shata ne a gidan marigayiya Hajiya Laraba Tashin Gobe da ke Zariya Road, a nan cikin garin Kaduna. Kimanin shekara 45 da suka wuce ke nan. Bayan nan, akwai wani otel da ake kira Common Wealth Hotel da ke kan Katsina Road, a nan ma muna haduwa da shi idan ya zo wasa. Daga nan sai ya koma yin wasa a Premier Hotel, amma duk da haka ba mu fasa zuwa kallon wasansa ba. Saboda a lokacin mu ba ma jin ciwon kashe kudi. Duk abun da muke yi idan muka ji zai yi wasa, za mu je, kuma za mu kashe masa kudi yadda ya kamata. Sai da ta kai ga matsayin ya ce na tsaya haka da ba shi kudi, duk wani abu da nake da bukata zai yi ba tare da na yi masa kyautar ko sisin kwabo ba, domin ya ga irin abubuwan da nake masa. Saboda Shata yana da wata dabi’a da idan ya ga kana masa alherin da zai wuce karfinka, to zai ce ya isa, ka dakata haka nan.
Aminiya: Kai kadai ya taba wa hakan?
A’a, ba ni kadai ya taba wa ba. Ka ga akwai wani da ake kira Alhaji Garba, shi ma ya taba ce masa ya daina ba shi kudi haka, domin gudun kar ya kure karfinsa.
Aminiya: Ko akwai wani abu da ke ba ka mamaki game da Shata?
kwarai kuwa. Saboda da zarar Shata ya taka kafarsa a garin nan, zai aika  gidan Hajiya Laraba Tashin Gobe don a kawo masa abinci. Ka san ita tana sayar da abinci ne. Idan kuma zai yi wasa akan tanadi sankira da zai kewaya domin sanar da jama’ar gari wurin da za a gudanar da wasan. Ka ga idan ranar ta zo, a nan ne kaina ke daurewa saboda mamaki. Za ka ga mutane kamar suna fitowa daga kasa. Wannan abun na ba ni mamaki matuka har yanzu.  Ka ga idan aka ce ga Shata ya iso, za ka ga yadda mutane suke tururuwar zuwa ganinsa kamar me. Abun da ke ba ni mamaki kuwa shi ne, Shata ba yana da wata halitta da ta saba wa sauran mutane ba ne, a ce ko kai biyu, ko wani kaho, ko ido guda hudu, shi mutum ne kamar kai. Amma inda ya bambanta da sauran mutane shi ne wajen basira da hikimar rera waka. Dalili da wannan sai na dauka akwai wata baiwa da Allah Ya yi mashi.  A gaskiya ban da Shata, ni a duk tsawon rayuwata, ban taba ganin mutum da Allah Ya yi wa irin wannan baiwar ba.
Aminiya: Wace kyauta ce ka taba yi wa Shata wadda ba za ka iya mantawa ba?
Akwai wata kyauta da na yi masa, wadda zan iya cewa kyautar shiga daka kai kuka ce. Kodayake kwalliya ta biya kudin sabu. Domin a gaskiya da ya samo ni, yana wake ni, a nan otel din Common Wealth, yadda ka san an sa mun kidan Gangi, saboda yadda nake tsananin tsima. debo kudi nake ina mikawa, har sai da aka zaunar da ni. Amma ban fahimci cewa mutumin da ya zaunar da ni masoyina ne ba, sai bayan da na koma gida na natsu. A gaskiya sai daga bisani ne da na dawo hayyacina, na gane cewa wannan mutumin mai kaunana ne.
Aminiya: Me kake tuna marigayin da shi?
A duk lokacin da na tuna da Shata, nakan tuna da irin kyakkyawar mu’amalar da muka yi da shi.
Aminiya: Idan muka koma kan sana’arka ta fawa, har yanzu kana yi kuwa?
Har yanzu ina sana’ar fawa, amma ba kamar yadda muka gudanar a baya ba, saboda yanzu girma ya zo mana. Kodayake duk da haka nakan sanya Kilishi a bayan motata domin kai wa masu bukata su saya, kuma cikin masu sayen har da Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero. Ina sana’ar ne saboda zama haka ba zai yiwu ba, musamman ma ganin cewa likita da kansa ya ce na dinga gudanar da kananan ayyuka domin motsa jinina.
Aminiya: Wace fa’ida ka samu a sana’ar fawa?
A gaskiya sai dai godiya ga Ubangiji, saboda duk abun da ake nema na rufin asiri Allah Ya yi mana. Ina da gidaje da motocin hawa da sauran kadarori da dama.
Aminiya; Kana da wani buri a halin yanzu?
 A gaskiya Alhamdulillah. Ka ga farko Allah Ya mana tsawon rai da lafiya saboda har yanzu ni nake tuka motata. Amma babban burina shi ne fatan cikawa da imani.
Aminiya: Ya batun iyali?
Ina da mata hudu da ’ya’ya 27 da kuma jikoki kimanin guda 55.