Kyautata dabi’u bayan watan Ramadan alamar karbuwar azumi ne – Shaikh Sautussunnah

Malamai da dama sun yi jan hankulan al’ummar Musulmi da su tabbata sun ci gaba da nuna kyayawan dabiu wadanda aka sansu da shi a lokutan Azumin Ramadan har izuwa bayan Azumi. Shaikh Amin Ibrahim Sautussunnah a zantawar sa da Aminiya ya shaida cewa kyautaya dabi’u bayan watan azumin Ramadan alama’ar karbuwar ibadun da aka […]

Kyautata dabi’u bayan watan Ramadan alamar karbuwar azumi ne – Shaikh Sautussunnah

Malamai da dama sun yi jan hankulan al’ummar Musulmi da su tabbata sun ci gaba da nuna kyayawan dabiu wadanda aka sansu da shi a lokutan Azumin Ramadan har izuwa bayan Azumi.

Shaikh Amin Ibrahim Sautussunnah a zantawar sa da Aminiya ya shaida cewa kyautaya dabi’u bayan watan azumin Ramadan alama’ar karbuwar ibadun da aka yi ne a lokacin watan Azumin, ya ce Allah madaukakin Sarki ya farlanta Azumin Ramadan ne domin al’umma su sami takawa.

“Ka ga wanda ya sami takawa dabiun sa za su zamo kyawawa har bayan watan Ramadan, domin su sahabbai sukan yi shekara guda cur dabi’un su gaba daya na Ramadan, domin suna kasance wa cikin watanni shida bayan Ramadan cikin juyayin rabuwa da shi kana watanni shida kafin zuwansa su na cikin bege da marmarin zuwansa don haka bayan watan Azumin Ramadan abu muhinmmi shi ne mu tasirantu da kyawawan ayyukan da muka gabatar da abin da Azumin ya karantar damu sannan mu yi kokari mu yi Azumi shida na watan Shawwal ga wanda Allah ya baiwa iko za a rubuta masa ladan ya yi azumi na shekara guda,” in ji shi.

Ya ce, Azumin na sitta shawal ya zo a hadisi ingantacce don haka duk wanda ya yi shi da kyakyawar niya ko a jere ko a rabe sai sami tarin lada tamkar ya azumci shekara guda.