La Liga: Barcelona ta yi wa Osasuna gida da waje a bana
Osasuna ta yi nasara a kan Barcelona a 2020.
Barcelona ta ci Osasuna 1-0 a wasan mako na 33 a gasar La Liga da suka kara ranar Talata a Camp Nou.
Jordi Alba ne ya ci wa Barcelona kwallon saura minti biyar a tashi daga karawar, inda hakan ya sa ta hada maki ukun da take bukata.
- Za a tsagaita wuta ta kwanaki 7 a rikicin Sudan
- NAHCON ta bayyana kamfanin jirgin da zai yi jigilar alhazan Kano
Osasuna ta karasa karawar da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Jorge Herrando jan kati a minti na 27 da fara tamaula.
Da wannan sakamakon Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da maki 82, ita kuwa Osasuna mai maki 44 tana ta tara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Ranar 9 ga watan Nuwambar 2022, Barcelona ta je ta ci Osasuna 2-1 a wasan farko a kakar bana da suka kara.
David Garcia ne ya fara ci wa mai masaukin baki, Osasuna kwallo a minti na shida da take leda.
Daga baya Barcelona ta zare ta hannun Pedri a minti na uku da komawa zagaye na biyu, sannan Raphinha ya ci na biyu, saura minti biyar a tashi wasan.
A karawar ce aka bai wa ’yan wasan Barcelona biyu jan kati, wato Robert Lewandowski da kuma Gerrard Pique, wanda ke zaune a benci.
Osasuna ta yi nasara a kan Barcelona a 2020, amma aka doke ta 4-0 a kaka biyu a jere da ta je Camp Nou.