La’antar shugabannin za ta dada jefa jama’a cikin kunci – Gwamna Gaidam

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce muddin al’umma suka ci gaba da jifar shugabannin da munanan addu’o’i na la’anta za su ci gaba da fuskantar munanan abubuwa daga wurin shugabannin. Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana haka ne a jawabinsa jim kadan da rantsar da shi da Babban Jojin Jihar Mai shari’a Garba Musa […]

La’antar shugabannin za ta dada jefa jama’a cikin kunci – Gwamna Gaidam
La’antar shugabannin za ta dada jefa jama’a cikin kunci – Gwamna Gaidam

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce muddin al’umma suka ci gaba da jifar shugabannin da munanan addu’o’i na la’anta za su ci gaba da fuskantar munanan abubuwa daga wurin shugabannin.

Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana haka ne a jawabinsa jim kadan da rantsar da shi da Babban Jojin Jihar Mai shari’a Garba Musa Nabaruma ya yi a babban filin wasa na 27 Augusta da ke garin Damaturu.
Gwamna Gaidam ya ce a yanzu babu abin da yake nema daga al’ummar jihar tunda sun sake zabensa a karo na biyu in ban da su ci gaba da yi masa addu’ar alheri ta samun jagoranci daga Allah ya samu damar gyara kura-kurensa na baya da sukunin shimfida mulkin adalci gare su. “Domin shugabanni addu’ar alheri ya kamata a rika yi musu ba mummunar addu’a ba mummunar addu’a ga shugabanni babu abin da za ta kara musu in ba sake ci gaba da kangarewa ba ta yadda za su ci gaba da azabtar da al’ummar,” inji Gwamnan.
Gwamnan ya ba da tabbaci ga al’ummar jihar cewa zai ci gaba da dorawa daga inda ya tsaya dangane da ayyukan raya kasa musamman kan abin da ya shafi kara inganta harkokin kiwon lafiya da ilimi da aikin gona da gina hanyoyi da samar wa da matasa aikin yi da kuma kara bada karfin gwiwa ga hukumomin tsaro don inganta harkokin tsaro a jihar.
A wani labarin Gwamna Gaidam ya nada Alhaji Abdullahi Bego a matsayin Daraktan Labaransa.
Wata sanarwa dauke da sa hannun mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar kuma Babban Sakatare a Gidan Gwamnatin Jihar Alhaji Baba Malam Wali da ta iso ga Aminiya ta ce nadin ya fara aiki ne nan take kuma shi ne nadi na farko da Gwamna Gaidam ya fara a zangonsa na biyu.
A shekarar 2007 ne Alhaji Abdullahi Bego ya fara rike wannan kujera ta Daraktan Labarai na Gwamna a zamanin marigayi Gwamna Mamman Ali, inda bayan rasuwarsa Gwamna Gaidam ya amince masa don ci gaba da rike wannan matsayi inda daga bisani ya kara ba shi matsayin mai bada shawara kan harkokin watsa labarai.