Labanon na tuhumar Yariman Saudiyya da safarar miyagun kwayoyi
A ranar Litinin da ta gabata ne hukumomi a kasar Labanon suka gurfanar da Yariman Gidan Sarautar Saudiyya tare da wasu mutum tara bisa tuhumarsu da fataucin miyagun kwayoyi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya bayyana.Rahotanni sun bayyana cewa an kama Yarima Abdel Mohsen Bin Walid Bin Abdulaziz da kuma wasu ’yan Saudiyya guda […]
A ranar Litinin da ta gabata ne hukumomi a kasar Labanon suka gurfanar da Yariman Gidan Sarautar Saudiyya tare da wasu mutum tara bisa tuhumarsu da fataucin miyagun kwayoyi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya bayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Yarima Abdel Mohsen Bin Walid Bin Abdulaziz da kuma wasu ’yan Saudiyya guda hudu ne a ranar Talatar makon jiya a filin jirgin saman birnin Beirut. Kamar yadda aka ruwaito an kama su ne da Hodar Ibilis da kuma wasu kwayoyi da nauyinsu ya kai tan biyu.
Wani jami’in kasar ya ce sun yi nasarar dakile wannan mummunar fataucin miyagun kwayoyin da ba a taba gani ba a tarihin kasar. Har ila yau, gidan talabijin din kasar Iran wato PRESS Tb da kuma Aljazeera sun ruwaito cewa kwayoyin da aka kama yariman da su irin su ne wadanda ’yan tawayen Takfiri suke sha a kasar Siriya don su kara kaimi wajen yaki.
A shekarar 2013 ne ofishin Majalisar dinkin Duniya Mai Kula da Yaki da Shan Miyagun kwayoyi ya ce yankin Gabas-ta-Tsakiya yana daya daga cikin yankunan da aka fi ta’ammali da miyagun kwayoyi.