Labarai daga Salihu Maqera Yunquri na qarshe da Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Bamanga Tukur ya yin a neman goyon bayan wakilan Babban Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP (NWC) na su goya masa baya dangane da yunqurin cire shi daga shugabancin jam’iyyar ya

Yunkuri na karshe da Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Bamanga Tukur ya yin a neman goyon bayan wakilan Babban Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP (NWC) na su goya masa baya dangane da yunkurin cire shi daga shugabancin jam’iyyar ya hadu da cikas, inda wakilai biyu ne kacal daga 12 suka halarci taron gaggawa da ya kira a […]

Labarai daga Salihu Maqera Yunquri na qarshe da Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Bamanga Tukur ya yin a neman goyon bayan wakilan Babban Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP (NWC) na su goya masa baya dangane da yunqurin cire shi daga shugabancin jam’iyyar ya

Yunkuri na karshe da Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Bamanga Tukur ya yin a neman goyon bayan wakilan Babban Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP (NWC) na su goya masa baya dangane da yunkurin cire shi daga shugabancin jam’iyyar ya hadu da cikas, inda wakilai biyu ne kacal daga 12 suka halarci taron gaggawa da ya kira a farkon makon nan.
Wakilan kwamitin biyu da suka halarci zaman su ne Sakataren Jam’iyyar ta kasa Farfesa Adewale Oladipo da Oditan Jam’iyyar ta kasa Alhaji Adewale Adeyanju, wanda hakan ya hana taron gudana saboda rashin cikar ka’idar yawan wakilai.
Taron an so ya gabaci na Babban Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a jiya Alhamis, wanda har hada wannan rahoto ba mu samu sakamakonsa ba.
Bamanga wanda ke fama da matsi kan ya sauka daga mukaminsa ya sha alwashin ba zai yi murabus ba, saboda zabensa aka yi kuma babban taron jam’iyyar ne kawai zai iya cire shi.
Tukur ya shaida wa manema labarai ta tarho cewa, “Ni ne zababben shugaban Jam’iyyar PDP na kasa. Ina da takardar shaidar zabena, ba zan sauka ba, babban taro ya zabe ni, don haka babban taron ne kawai zai sauke ni.”
Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa Bamanga ya kira taron ne domin warware wasu matsaloli da suka shafi wakilan, lamarin da ya sa suke fusace da shi, ta yadda in za goya masa baya idan batun ya sauka ya taso a taron na jiya.
Wakilan Kwamitin NWC wadanda suka gana da Shugaba Jonathan a makon jiya, an ce sun koka game da jiji da kan Bamanga wajen gudanar da harkokin jam’iyyar. An ruwaito cewa sun ce Bamanga bai tuntubarsu a muhimman shawarwari, inda ya fi gudanar da harkokin jam’iyyar a gidansa.
Akwai bayanan da ke cewa wakilan NWC sun yi haka ne domin goya baya ga wasu gwamnonin PDP da suke neman a cire Bamanga Tukur daga shugabancin jam’iyyar domin ceto ta daga rugujewa baki daya.
Gwamnonin PDP biyar sun fice daga cikinta a watan Nuwamban bara, yayin da ’yan Majalisar Wakilai 37 suka bi bayansu, kuma a makon jiya tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wasika ga shugaban jam’iyyr ta kasa cewa ya janye jikinsa daga harkokin jam’iyyar.