Labaran ma’aurata: Na rufa masa asiri sai na tarar da farin ciki
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin:
Assalamu alaikum Anti Nabilah, ni ma ga labarin aurena: Na girma a wajen matar babana domin mahaifiyarmu ta bar gidan mahaifina tun ina ciki. Bayan ta yaye ni aka dawo da ni gidan mahaifina. Na sha matsaloli da wahalhalun da aka saba na rikon kishiya.
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan banga 5 a Neja
- An kama matashi da laifin yi wa ‘yar shekara 75 fyade a Anambra
Ko sakandare ban gama ba, matar babana ta sa aka yi min aure da wani dan uwanta, kawai domin mahaifinsa mai kudi ne kuma shi kadai ne dansa namiji. Muna zaune lafiya da mijina, mutum mai tsananin kirki da kyautatawa. Komai nake bukata yana yi min.
Sai da muka shekara biyar bai taba neman kusanci irin na aure da ni ba. Tun ban fahimci me ke faruwa ba saboda karancin shekaru har na fahimta. Bayan shekara bakwai ban samu ciki ba balle in haihu, sai mutane suka fara surutu musamman dangin miji, suna kirana juya marar haihuwa.
Ba kamar matar babana da kuma uwar mijina, wacce ta yi matsin duniyar nan a kan danta ya kara aure ya ki yarda, sai take cewa wai na shanye mata da da asiri kuma na ki haihuwa. Kullum cikin wulakanci da cin fuska nake daga gare ta.
Ban taba gaya wa kowa halin da aurena yake ciki ba, ko mahaifiyata da take yawan zuwa tana kawo mani magungunan wankin mara da gyaran mahaifa ban taba ce mata ga matsalar da ke faruwa ba. Wata rana a gidan sunan dangin miji, yayar miji da uwar miji suka yi mani wulakanci da cin fuska na wuce iyaka.
Na dawo gida ina ta kuka. Na kasa barci a wannan daren. Maigidana ya zo ya same ni yana ta rarrashina.
Ya ce wata kanwarsa ta sanar da shi duk abin da aka yi min a gidan sunan. Ya ce da ni: “Wance ina da matsalar mazakuta, don Allah ki rufa min asiri kada ki bari duniya ta san cewa ni ban cika namiji ba. Ki yi hakuri duk wanda ya yi hakuri karshensa dimbin farin ciki.”
Haka muka ci gaba da zama har tsawon shekara goma sha biyar. Wata rana mahaifiyarsa ta kwanta rashin lafiya, tana jinyar ta kira shi ta ce ko ya kara aure, ko ya sake ni ko ta tsine masa.
A nan ne fa dole ya gaya mata cewa ga matsalarsa ta rashin mazakuta saboda wani ciwo da ya shafi marainansa. Bayan ta warke ta zo har kuryar dakina tana kuka ta roke ni in yafe mata. Daga nan ta rika kyautata min tana ji da ni matuka fiye da yadda take ji da ya’yanta.
Kowa ya yi mamakin wannan al’amari musamman mahaifiyata wacce ta yi, ta yi, da ni in sanar da ita abin da ke faruwa na ki sanar da ita. Wannan ya sa (da ta ji) ta tayar da fitina ta ce dole sai dai mijina ya sake ni in je in yi wani aure.
Daga karshe ta kai kara kotu. Wannan ya sa dole mijina ya sake ni yana kuka ina kuka muka rabu.
Bayan na gama idda, ba tare da sanin kowa ba tsohon mijina ya turo wani abokinsa da ke zaune a kasar Saudiyya ya aure ni na koma can da zama, inda yanzu haka ina da ’ya’ya biyar kuma ina zaune lafiya da mijina da abokiyar zamana.
Tsohon mijina ya ki ya kara yin wani aure, wanda hakan ya rika sosa min zuciya.
Har sai da Allah Ya ba ni dama na sama masa wata baiwar Allah kyakkyawa kuma cikakkiyar mace daga waje amma a ciki ita ma tana fama da irin lalurarsa, domin an haife ta da kofar ’yan matanci da ba ta gama budewa ba, sai da aka yi mata aiki wajen sau hudu sannan ne ta samu take yin fitsari ba tare da matsala ba.
Kuma yanzu haka suna da yara uku da suke daukowa daga gidan marayu, tun suna jarirai su raine har su girma a gabansu. Lallai duk wanda ya rufa wa wani asiri shi ma Allah zai rufa masa nasa kuma karshen hakuri farin ciki.
Sai makon gobe…