Labaran Maku ya bijire mini – Jonathan

Shugaba kasa Dokta Goodluck Jonathan ya musanta kalaman da tsohon ministansa na yada labarai kuma dan takaran Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APGA Mista Labaran Maku ke yi cewa Jonathan ne ya umurce shi ya canja sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APGA don ya mara masa baya.  Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne lokacinda […]

Labaran Maku ya bijire mini – Jonathan
Labaran Maku ya bijire mini – Jonathan

Shugaba kasa Dokta Goodluck Jonathan ya musanta kalaman da tsohon ministansa na yada labarai kuma dan takaran Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APGA Mista Labaran Maku ke yi cewa Jonathan ne ya umurce shi ya canja sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APGA don ya mara masa baya. 

Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne lokacinda yake jawabi a wajen yakin neman zabensa a garin Lafiya fadar Jihar Nasarawa, inda ya bayyana Labaran Maku a matsayin maci amana da a cewarsa ya amince da shi amma daga bisani ya bijire masa da Jam’iyyar PDP ta hanyar canja sheka daga PDP zuwa APGA ba tare da ya sanar da shi ba.
Shugaba Jonathan ya ce shi cikakken dan PDP ne saboda haka ba ya da wani dan takarar kowace kujera daga wata jam’iyya da zai goya masa baya, in ba PDP ba.
Shugaban Jonathan ya yi alkawarin cewa har idan al’ummar jihar suka sake ba shi dama gwamnatinsa za ta hada hannu da gwamnatin jihar wajen bunkasa noma da dimbin ma’dinai da Allah Ya albarkaci jihar da su.
Sai ya bayyana wasu ayyukan da gwamnatinsa ta yi wa jihar da suka hada da gina jami’ar tarayya a garin Lafiya da ofishin babban bankin Najeriya da kamfanin sarrafa shinkafa na zamani a garin Doma da sauransu.
Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu bayan ya mika wa Alhaji Yusuf Agabi tuta a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar a inuwar jam’iyyar ya yi kira ga al’ummar jihar su fito kwansu da kwarkwata su zabi Yusuf Agabi don ba shi damar samar musu da ainihin ribar dimokuradiyya.
A jawabinn Alhaji Yusuf Agabi ya yi alkawarin kwato mulkin jihar daga hannun Jam’iyyar APC wadda a cewarsa ta sace ragamar mulkin jihar ne daga hannun PDP da ke mulkin jihar tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999.