Labari kan kadara da jarin da ake gudanar da kasuwanci

Wani matashi ya tambayi mahaifinsa, me zan yi in zama dan kasuwa wanda zai samu nasara? Mahaifinsa ya kyale shi ya yi dariya ya kamo wuyansa ya zaunar da shi, su biyun suka zauna. Sai babansa ya gaya masa karamar hanyar samun nasara. Akwai wasu mata guda biyu, daya tana da digiri daga wata babbar […]

Labari kan kadara da jarin da ake gudanar da kasuwanci

Chukwuma Nwanze

Wani matashi ya tambayi mahaifinsa, me zan yi in zama dan kasuwa wanda zai samu nasara? Mahaifinsa ya kyale shi ya yi dariya ya kamo wuyansa ya zaunar da shi, su biyun suka zauna. Sai babansa ya gaya masa karamar hanyar samun nasara.

Akwai wasu mata guda biyu, daya tana da digiri daga wata babbar jami’a sunanta Zeo ita kuma daya matar sunanta Zara wacce ba ta je jami’a ba  amma ta koyi yadda ake saye da sayarwa wajen mahaifiyarta. Zeo da Zara suka yi tunanin fara kasuwanci daga abin da suka koya Zeo ita ta kware wajen gasa burodi kuma ta yi tunanin fara gasa burodi ita kuma Zara ta iya girki don haka ta ce za ta fara gidan abinci. Kafin su rabu daga gida, Zeo an ba ta kudi daga gida kuma ta samu rance daga babbar kawarta Zikora wanda za ta biya bayan wata shida, Mahaifiyar Zara ta nemi rance na wata shida daga kungiyar wurin aikinta ta sayar da wasu kayayyakinta ta hada ta bai wa Zara.

Zeo ta zabi ta yi kasuwancinta kusa da makwabtanta da yake yawancin masu zama sun zabi su zauna wajen da ingancin lafiyarsu zai gudana kuma da yawansu suna fita motsa jiki kowace safiya. Don haka ta samu wuri a kan babbar hanya a bakin titi kusa da wasu manyan shaguna ta samu ta kawata wajen ta rubuta sunan “Zeo”  bayan gama tsara ciki da wajen gidan burodin, Zeo ta shirya sayen kayan sarrafa burodin domin ta tabbatar ta saye duk abin da ta kashe wajen gyara shagon da biyan haya ta gyara wajen ajiye burodin mai makon ta sayi sabo sai ta sayi tsoho da kudin da ya rage ta hada  cin abinci da liyafa ta samu yin rawa da abokanta, sun yi rawa kuma suka tura hotuna a shafuka sada zumunta na Intanet a kowane dare.

Zara ta samu  cancantar damar bude wajen cin abinci kusa da wajen hada-hadar  garejin shiga mota inda kullum daruruwan mutane ke shiga mota. An yi amfani da sunanta aka ba shagonta, tana abincin gargajiya da na zamani za ka iya ci ko azuba ka tafi da shi. Tana tabbatar da kullum shagonta a tsabtace yake kuma tana tabbatar da yaran shagonta suna kula da abokan huldarta. Ta saka jarinta bakin gwargwado don tafiyar da shagon abinci kuma ta saya abin da take bukata da niyyar nan gaba za ta ci gaba da sayen sauran kayan idan ta ga ci gaban kasuwarta.

 

Duk harkar kasuwanci ta kankama kusan lokaci daya, bayan wata uku da fara gasa burodi, Zeo ta fara korafi kan masu sayen kayanta ba kamar yadda ta yi zato ba. Kawarta koyaushe takan zo tana jin dadin ta ba da kyautar burodi ga kawayenta idan za su tafi koda sun yi niyyar saye da kudinsu, sukan sayi bashi a mafi yawan lokuta. Injin gasa burodin ya fara ba ta matsala har ba ta yin burodin wata rana. Ta fara samun matsala da masu aikin cikin shaguna, suna so ta biya su kudin wata uku nan gaba. Zeo ta samu damuwa, komai yana yin kasa. Komai ya yi kasa. Ba ta biya rancen da ta dauka ba, ba kudi, ba masu sayen kaya, lalatattun injina kuma ga karin kudin shago ina makomarta ta dosa?

Zara kuwa ta samu kasuwa, inda take cin kasuwar dafa shinkafa da mutane na kusa da na nesa ke zuwa sayen dafa-duka. Ta sa tsarin biyan kudi kafin a ba ka abinci. Yarinyar shagonta ke zuba abinci inda ita kuma take karbar kudi. Tana biyan kudin da aka sa mata na rancen da mahaifiyarta ta ci saboda ita da za ta fara kasuwanci. kasuwancinta ya samu karbuwa.

Don haka yaron ya ji dadin labari lokacin da mahaifinsa ya tambaye shi idan ya karu da wani abu a kan wannan takaitaccen labari. Lokacin da yake kokarin ba da amsa, mahaifin ba ya ci gaba da cewa, idan kana so ka zama wanda ya ci gaba a kan kasuwanci, kana bukatar ka san muhimmanci kayanka, kudin kamfaninka wanda za a biya ka ta hanyar mayar da kudinka a cikin kasuwanci. Ya ci gaba da cewa kana bukatar sanin kadarorinka, kudin kamfani da za a biya ka da kudinka a cikin kasuwanci. Tambayar kididdigar lissafi (kadarorinka-kudinka da za ka mayar-kudinka a cikin kasuwanci) idan ka san su duka, za ka iya mallakar kadara idan ka mayar da kudin ko kudin da ke ciki ko kuma idan ka hada su gaba daya. Kadarori za ka iya cewa su ne kayayyakin da kake sarrafawa wajen kasuwanci wanda nan gaba za ka amfana daga kasuwancinka “Ribar da za ka samu a gaba” daga wannan takaitaccen bayani kan hanyar samar da kudin kasuwanci ya isa ka gane wannan kawai zai samar da kudaden shiga. Kudinka na waje zai zama abin da za ka rike, a matsayin kasuwancin da ka fara wanda idan aka biya ka zai zama wani ci gaba na kasuwancinka”. Kudi na cikin kasuwancinka shi ne kamar jarin kasuwanci ainihin kadararsa kuma shi kadara a cire kudin da ba su a hannunka. kudinka na waje shi ne kudi a hannu wanda za ka fara kasuwancinka.

Kadara ita ce za ka iya mallaka wajen aro ko (rance daga wajen ’yan uwanka ko abokanka) shi kuma kudinka (kamar ajiyarka, kudin da ka gada ko kudin abokinka da sauransu) abin da yake cikin rance ko kudinka shi ne abin da ka mallaka kadararka (ka sani cewa kafin lokacin da za ka fara, kudin da za ka biya ko kudin za ka iya amfani da shi don sanin kudinka) kadara zai samar da hanyar samun kudi lokacin da za a fara gudanar da kasuwanci. Shi ne kudin da za a juya  a kuma biya kudaden da aka yi aikace-aikace lokacin da aka bukata haka. Idan aka samu raguwar kudi sai a sayi wata kadarar, a yi amfani da shi don cigaban kasuwanci, ko don cigaban kasuwanci ko abiya masu hannun jari.

Ya yi kamar ya rude, yaron ya tambayi mahaifinsa, yaya aka yi duk suka shafi wannan bayani?  Mahaifin  ya amsa masa da cewa:

  1. Kudin da Zeo ta samu daga iyayenta ita kuma Zara daga na kungiyar mahaifiyarta don haka kowane kasuwanci yana bukatar kudi yana nuna yunkurinka da yadda da kasuwanci da za ka yi a fili ke nan.

2- Kudin da Zeo ta ranta wajen Zikora da na mahaifiyarta da ta amsa suna bukatar a biya yayin kasuwanci, za a biya wani abu ciki karkashin rancen. Fara karamin kasuwanci yana bukatar ka sa kudi cikinsa a yayin farawa a lokacin da ka fara tara kudi a kai-a kai, ka iya karbar rance idan kana bukata a lokacin.

3- Idan kana so ka zama dan kasuwar da ya bunkasa. Kana bukatar fiye da dabaru. Zeo da Zara suna da baiwa a kan abin da suke yi amma Zara ta nuna ta fi iya tafiyar da kasuwanci.

  1. Kudi suna tare da rayuwar mutum na duk wata ma’aikata. Duk kasuwancin da ba issashen kudi ko kadan, ko madaidaici, ko babba lokaci, da kudi ne za ka yi al’amuran kasuwanci yau da kullum, ka biya rance, ka rage wani abu don gudanar da aiki, ka sa jari, ka mallaki kadarori kuma lokacin ba da riba
  2. Wanda ya fahimci kasuwarsa da abin da yake samar yake yi da kudin kaya, ci gaba da wurin kasuwanci shi ne mafi girman fahimta, jari da abin da kake so duk dan kasuwa yana da shi.

Mahaifinsa ya tambayi dansa, ka samu wani abin da ka karu da shi? “Yaro ya ce, kasuwanci zai inganta lokacin da abokai da ’yan’uwa suka biya kudin kaya”