Labarin Aku (2)
Barkan mu da warhaka Manyan Gobe. A yau zan kawo muku barshen Labarin Aku ne da na fara kawo muku a makon jiya. Ina fata kuna biye da mu don jin yadda labarin zai kare. Na san Manyan gobe kun bosa ku ji barashen wannan labari. Bayan Mayyar ta shabe wuyan Akun ya mutu […]
Barkan mu da warhaka Manyan Gobe. A yau zan kawo muku barshen Labarin Aku ne da na fara kawo muku a makon jiya. Ina fata kuna biye da mu don jin yadda labarin zai kare. Na san Manyan gobe kun bosa ku ji barashen wannan labari.
Bayan Mayyar ta shabe wuyan Akun ya mutu sai ta bar gidan, ba ta zame ko’ina ba sai fadar Sarki.
Abin mamaki a lokacin da ta isa fadar Sarki sai ta ci karo da wani Aku wanda suka yi kama da wanda ta murde wa wuya a gidan maharbi. Da farko abin ya ba ta tsoro amma da ta lura da kyau sai ta ga kama ce kawai a tsakanin wadannan Akun biyu.
Sai dai abin da ya ba ta sha’awa da kuma burge wa shi ne yadda wannan Aku da ke gidan Sarki ya tarbe ta da hannu bibbiyu, inda ya riba yi mata kirari da fada mata kyawawan maganganu. Abin ya ba ya burge ta.
Nan da nan ta budc jakarta ta yi wa Akun kyauta mai yawa kuma ta shaida wa Sarki a riba kula da wannan Aku da kyau don ya san mutuncin babi.
Aku ya karbi kyauta daga Mayya inda ya yi mata godiya.
Manyan gobe da fatan kun koyi darasi daga wajen wadannan Aku guda biyu. Daya ya koyi rashin kunya da hakan ya janyo masa ajali, yayin da dayan kuma ya koyi da’a da biyayya da hakan ya janyo masa daukaka.
Da fatan Manyan gobe za su kasance masu ladabi da biyayya a duk inda kuka tsinci kanku.