Labarin Audu mai mako
Barka da warhaka Manyan Gobe Assalamu alaikum Manyan Gobe Yaya karatu? Fatan alheri gare ku. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Audu mai mako’. Labarin na kunshe ne da yadda mako ya sanya Audu ya halaka. A sha karatu lafiya.Taku: Gwaggo Amina Abdullahi. Labarin Audu mai mako Malam Audu […]
Barka da warhaka Manyan Gobe
Assalamu alaikum Manyan Gobe
Yaya karatu? Fatan alheri gare ku. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Audu mai mako’. Labarin na kunshe ne da yadda mako ya sanya Audu ya halaka.
A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi.
Labarin Audu mai mako
Malam Audu mutum ne mai tattali da mako. Ba ya sha’awar yi wa kowa kyauta, idan kana so ka ga bacin ransa ka roke shi kudi. Ga shi kuma yana da dimbin dukiya.
Rannan an yi ruwa da daddare ga duhu ya mamaye ko’ina ya zo wucewa sai ya fada rijiyar gidansa. Ya yi ihun neman taimako. Can sai matarsa A’isha ta ji ihunsa ta kuma nufo bakin rijiyr. Bayan ta karaso bakin rijiyar “Lafiya Malam ya aka yi ka fada cikin rijiya?” Sai ya ce: “ki nemi igiya ki ciro ni.”
Bayan ‘yan mintuna saita zo da wata katuwar igiya. Ta wurga masa domin ya kama.
Bayan ya ga kyawun igiyar sai ya ce “Aisha a ina kika samo wannan igiyar mai matukar kyawu?” Sai ta ce “na sayo ta ne dubu daya a shagon Malam Garba.”
Jin haka sai ransa ya baci ya ce ta je ta sayo ta naira 150 a shagon Malam Tanko. Kuma ta yi sauri kada ya nitse.
Koda ta dawo ta yi ta kiran Malam Audu sai ta ji shiru. Ashe bayan ta tafi sai ruwan rijiyar ya karu har ya nitse cikin ruwa.
Da fatan Manyan Gobe za su zama masu kyauta kuma su guji yin mako.