Labarin Audu mai taurin kai
Barka da warhaka Manyan GobeBarkanmu da warhaka Manyan Gobe. Da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Audu mai taurin kai’. Labarin na kunshe da yadda ya kamata Manyan Gobe su zama masu natsuwa da kuma bin iyaye, domin an ce ‘wanda bai ji bari ba, zai ji hoho’. A sha karatu lafiya.Gwaggwonku: […]
Barka da warhaka Manyan Gobe
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Audu mai taurin kai’. Labarin na kunshe da yadda ya kamata Manyan Gobe su zama masu natsuwa da kuma bin iyaye, domin an ce ‘wanda bai ji bari ba, zai ji hoho’. A sha karatu lafiya.
Gwaggwonku: Amina Abdullahi
Labarin Audu mai taurin kai
Akwai wani yaro mai suna Audu. Yana son cin kwallon yazawa (kashu) sosai. Kullum sai ya rika damun mahaifiyarsa ta ba shi kwallon yazawa. Idan ta ba shi sai ya ce ta kara masa. Wannan al’amari yana matukar damunta.
Rannan sai ta ce masa: “Audu, ya kamata ka rage cin kwallon yazawa domin idan ya yi yawa zai yi maka lahani.” Sai ta boye sauran kwallayen yazawa, sannan ta tafi kasuwa.
Da Audu ya ga mahaifiyarsa ba ta nan, sai ya je ya sayo kwallon yazawa ya rika ci.
Washegari, sai ciwon ciki ya kama shi. Bayan mahaifiyarsa ta kai shi asibiti, sai likita ya ce Audu ya kamu da ciwon ciki sakamakon yawan cin kwallon yazawa da ya yi, inda a yanzu hakan ya yi masa lahani a cikinsa.
Da fatan Manyan Gobe za su samu darasi daga wannan labarin. Da Audu ya ji maganar mahaifiyarsa, da bai yi ciwon ciki ba.