‘Labarin Biri da Kada’

Taku; Amina Abdullahi An yi wani Biri a wani daji wadda akwai rafi da kuma tsuntsaye da dama a cikinsa. Biri ya kasance kullum akan wata itacen zuma da kayan dadi. Duk dabban da ya yi wanka a rafin, sai biri ya tsinko masa kayan dadi a bishiyar da yake. Rannan Kada ya fito daga […]

‘Labarin Biri da Kada’

Taku; Amina Abdullahi

An yi wani Biri a wani daji wadda akwai rafi da kuma tsuntsaye da dama a cikinsa. Biri ya kasance kullum akan wata itacen zuma da kayan dadi. Duk dabban da ya yi wanka a rafin, sai biri ya tsinko masa kayan dadi a bishiyar da yake.

Rannan Kada ya fito daga cikin ruwa domin neman abinci. Ya shafe wajen awa daya a tsaye, amma ya kasa samin abin da zai kashe ya ci.

Ganin hakan ya sanya Biri ya kira Kada daga saman bishiya, sannan ya wurgo masa abinci daga sama. Kada ya yi godiya sosai ga Biri.

Kasancewar kirkin da Biri ya yi wa Kada yasa Kada ya shiga zuwa wajen Biri cin abinci da kuma hira har suka shaku sosai.

Kada na isa gida sai ya baiwa matarsa kayan dadin da Biri ya bayar a kawo mata. Ta na cin abincin ta ce da dadi kila zuciyar Biri tafi haka dadi don haka tana son zuciyar Biri.

Kada ya ce ba zai iya ba domin Biri amininsa ne. Matar Kada ta ki yarda har sai da ta ci galaba akansa.

Washe gari Kada ya je bakin bishiya kamar kullum. Ya ce da Biri ya sauko daga bishiya domin yasan gidansa. Biri ya ce ai “gidanka na cikin ruwa ni kuma ban iya ruwa ba”. Sai Kada ya ce zai goya Biri a bayansa.

Bayan sun kai tsakiyar rafi sai Kada ya ce ai kashe shi zai yi domin matarsa take son cin zuciyarsa. Biri ya ki nuna ya tsorata, sai ya ce ai ya baro zuciyar akan bishiya sai dai ya mayar da shi su dauko.

Suna isa bakin rafi Biri ya daka tsalle ya haye saman bishiya ya ce da Kada “mayaudari”.