Labarin Ese: Akwai jan aiki a gabanmu

batancin da cin mutunci da wasu kafafen watsa labarai ke yi a kan maganar Ese Oruru da Inusa Yellow kabilanci ne da siyasa. Hakan na haska wa duk wani mai tunani da hankali cewa. Maganar da ake na “Najeriya kasa daya al’umma daya” karya ne, a baki ne kawai da takarda. A zahiri kowa Ya […]

Labarin Ese: Akwai jan aiki a gabanmu
Labarin Ese: Akwai jan aiki a gabanmu

batancin da cin mutunci da wasu kafafen watsa labarai ke yi a kan maganar Ese Oruru da Inusa Yellow kabilanci ne da siyasa. Hakan na haska wa duk wani mai tunani da hankali cewa. Maganar da ake na “Najeriya kasa daya al’umma daya” karya ne, a baki ne kawai da takarda.
A zahiri kowa Ya san abin da ya faru a fili, ba ta yadda za a sato mutum, kuma wanda ya yi satar ya bayyana wa hukuma. Ese ta yi ikirari da kanta cewa ba sato ta aka yi ba. Don radin kanta ta biyo shi, hasalima da kudinta ta biya wa kanta kudin motar zuwa Kano. Amma abin takaici sai ga shi wasu kafofin watsa labarai na jujjuya labarin da cakuda shi don cimma buri kan su na kabilanci da siyasa a kan Musulunci da Musulman Arewa. Ta wani fannin hakan na nuna mana jan aiki da kalubalen da ke gaban al’ummar Musulmin Arewa, Talakawa, masu kudi da shugabanin al’ummar Musulmin Arewa, cewa, mun yi sakaci kuma muna cikin sakacin.
An bar mu a baya, an yi mana babbar rata ta fannin ilimi, iya kirkirar farfaganda a kafafen watsa labarai, ko kare kanmu daga farfaganda. Da tafiyar da rayuwa daidai da zamani. Hakan na da nasaba da yadda muke sakaci da harkokin ilimi.
Duba da kididdigar alkaluman daliban da suka rubuta jarabawar (Jamb) a wannan shekarar ta 2016.
Abin takaici da ban haushi duk yawan matasan Jihar Kano da ake ikirari da su, ba su kama kafar daliban Jihar Imo ba. Wannan wane irin ci baya ne?
Abin ban haushi da takaici da a shaye-shaye ne matasan mu ne a kan gaba. Wannan wani babban madubi ne da ke hasko makomar rayuwar matasan Arewa a nan gaba. Muddin ba mu tashi tsaye ba mun daina yaudarar kanmu, yanzu aka fara ci mana mutunci. Nan gaba ko tari Musulmin Arewa bai isa ya yi ba a Najeriya, saboda raini.

Mansoor Said PRP KANO. 07039215954. [email protected]

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya