Labarin Giwa
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau zan kawo muku labarin ‘giwa’ ne. Labari ne da ke nuna kada a rika nuna wa masoyi kiyayya. A sha karatu lafiya Akwai wata giwa ce a wani daji. Kadaici ya dame ta. Wata rana ta je ta iske biri ta […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau zan kawo muku labarin ‘giwa’ ne. Labari ne da ke nuna kada a rika nuna wa masoyi kiyayya. A sha karatu lafiya
Akwai wata giwa ce a wani daji. Kadaici ya dame ta. Wata rana ta je ta iske biri ta ce tana so su rika yin zumunci. Biri ya kwashe da dariya ya ce “haba giwa ai kin yi min girma. Kuma ba za ki iya hawa bishiya kamar yadda muke hawa ba, don haka sai ki kara gaba ni ban amince ba.
Abin ya bata wa giwa rai sai ta je ta samu zomo shi ma ta shaida masa ko zai yarda su kulla abota? Zomo ma ya kyalkyalce da dariya ya ce “hmn ai kin yi min girma don haka ya ki amincewa da bukatarta na yin abokantaka.
Ana cikin haka, sai giwa ta ga namomin daji suna gudu suna buya. Da ta tambayi dalili sai aka ce mata ai kura ne ta shigo dajin kuma tana kashe duk namun dajin da suka yi ido hudu.
Sai giwa ta samu kura ta ce ta daina kashe mata abokai. Kura ta ce “babu ruwanki giwa”. Sai giwa ta tsoratar da kura har ta gudu ta bar dajin ba shiri.
Daga nan sauran namun dajin suka fito daga wurin buya kuma suka rika yi wa giwa godiya. Sannan suka ba ta hakuri inda kowanensu ya nemi su yi abota.
Sai mako na gaba.
Taku; Gwaggo Amina Abdullahi.