Labarin Hannatun Keffi

Barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon zan fara kawo muku labarin Hannatun Keffi (ba sunanta na gaskiya ba), ina fata za ku bi ni sau-da-kafa don fahimtar darussan da labarin yake koyarwa. A sha karatu lafiya: A ranar wata Asabar da misalin karfe 11:00 na safe ne wani abokina dan jarida […]

Labarin Hannatun Keffi

Barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon zan fara kawo muku labarin Hannatun Keffi (ba sunanta na gaskiya ba), ina fata za ku bi ni sau-da-kafa don fahimtar darussan da labarin yake koyarwa. A sha karatu lafiya:

A ranar wata Asabar da misalin karfe 11:00 na safe ne wani abokina dan jarida mai suna Hashim Ibrahim ya kira ni, bayan na amsa kiran ne muka gaisa, sannan ya bukaci in raka shi gidan yari da yammacin ranar don ya gudanar da wani da gidan rediyonsu ya sanya shi. Duk da cewa na shirya da yammacin ranar zan rubuta wa Mujallar Weekend Magazine da ke fitowa a jaridar Daily Trust wani labari a kan dan fim din Kudancin Najeriya Nkem Uwoh wanda aka fi sani da lakabin Osuofia, amma sai ban fada masa ba, ban san dalilin da ya sa na kasa fada masa, daga baya na gane al’amarin da Allah Ya kaddara faruwarsa a gidan yarin ne ya sanya na kasa fada masa.
Da misalin karfe 4:00 na yamma sai na ji sautin motarsa a kofar gidana, na gane hakan ne kasancewar duk lokacin da ya zo wurina kafin ya yi wa motarsa matsugunni sai ya taka motar ta yi gunji tukunna. Ban jira ya yi sallama ba, na fito sanye da doguwar koriyar riga, da ma na kammala shiryawa, kasancewar na san shi mutum ne da yake cika alkawari. Bayan na fito na gan shi sanye da jar hula, a nan na fara zolayarsa ko za mu je tallar Kwankwasiyya a gidan yari ne. Bayan ya kalle ni sai ya yi dariya, kamar zai ce wani abu sai ya yi shiru, daga bisani ya ce na shiga mu wuce tun da mun yi latti.
Bayan mun kama hanya ne sai ya sanya mana wakar Sarkin Kano wadda Alan waka ya rera, haka muka ci gaba da tafiya har muka isa gidan yarin. Bayan mun cika dukkan ka’idojin ziyartar gidan yari aka hada mu da wani gandiroba wanda ya zama mana jagora. Ya ci gaba da nuna mana duk wurin da muka bukaci zuwa. Muna cikin tafiya muka iso bangaren mata, kallo daya na yi wa wata yarinya sai na ji hankalina ya tashi, dalili kuwa shi ne saboda karancin shekarunta, bugu da kari fuskarta ta kumbura, idanunta sun yi jajawur kamar garwashin wuta, ba ya ga haka ta rame kamar kudin guzuri. Ita kadai take zaune cikin zulumi da jimami, yawancin matan da suke wurin walwalarsu ta dara tata. Haka ya sanya na sake mayar da hankalina wurinta.
Ganin ina kallonta ne ya sanya ta kalle ni, a lokaci guda ta dauke kallonta daga gare ni zuwa kallon dan karamin yatsarta na hannunta na hagu. Haka kawai na ji tausayinta ya kammala ratsa zuciyata, kiran sunana da Ibrahim ya yi ne, ya ankarar da ni, daga baya na gane ashe sun ba ni tazara. Maimakon na bi bayansu sai na kira sunansa, ya tsaya a lokaci guda ya juyo, bayan ya kalle ni sai na yi musu alamar su zo. Bayan ya dan yi jim hade da murtuke fuska ne sai ya nufo inda nake, gandiroban bai yi gardama ba ya biyo bayansa, na yi mamakin hakan, amma daga baya na gane shi da Ibrahim sun san juna, hasalima unguwarsu daya a Kano.
Bayan sun karaso wurin da nake ne na nuna masa yarinyar da daga baya na gane sunanta Hannatu. Kallo daya Ibrahim ya yi mata na gane ya kagu ya san dalilin laifin da ta yi har aka yanke mata hukuncin dauri a gidan yari. Ganin muna kallonta ne ya sanya ta tashi daga wurin zuwa bangon daki na barin gabas.
Za mu ci gaba in sha Allah.