Labarin Hannatun Keffi (3)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A makon jiya mun tsaya a wurin da Bashir ya kasa barci mai inganci saboda halin da ya ga Hannatu ke ciki a gidan yari. A wannan makon za mu ci gaba daga wurin da muka tsaya. A sha karatu lafiya Washegarin tun da wuri na […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A makon jiya mun tsaya a wurin da Bashir ya kasa barci mai inganci saboda halin da ya ga Hannatu ke ciki a gidan yari. A wannan makon za mu ci gaba daga wurin da muka tsaya. A sha karatu lafiya
Washegarin tun da wuri na kammala duk wani shirina, sannan na shiga zumudin zuwan lokacin da aka sanya zan gana da Hannatu. Tun saura awa biyu lokacin ya cika ina kusa da gidan yarin. Saura minti talatin lokaci ya cika ina cikin gidan yarin. Na cika dukkan ka’idojin da ake bukata, sannan na fara da ganawa da Hassan. Muka ci gaba da hira har lokacin ziyara ya yi.
Hassan ne ya yi mini jagora zuwa dakin ganawa da ke gidan yarin. Madaidaicin daki ne mai dauke da tebura goma; kowane teburi zagaye yake da kujeru. Bayan mun isa dakin ne na zauna a daya daga cikin kujerun, sannan na ci gaba da kallon dakin daga bangare zuwa bangare.
Ganin na zaune sai ya ce bari ya taho da ita. Na ci gaba da zama cike da zamudi. Haka kawai sai na rika jin kamar takun sawunsu ne, sai na saurara sai na ji kunnuwana ne suke ruda ta. Me ya sa suke yi mini haka? Ni ma ban sani ba. Ban jima ina cikin zumudin ba ne, sai na ga sun shigo dakin; Hassan na gaba, Hannatu na biye da shi. Tun bayan da muka hada ido ne sai ta ci gaba da tafiya kanta a sunkuye. Na ci gaba da kallonta har lokacin da Hassan ya yi mata umarnin ta zauna a wata kujera da ke fuskantar kujerata.
Bayan ta zauna ne sai muka sake hada idanu, sannan ta sake sunkuyar da kanta. A nan Hassan ya tsaya a gefe. Bayan na yi gyaran murya, a lokaci guda na tafiyar da kallona kai-tsaye ga fuskarta ne, na fara magana: “Ita rayuwa ba yadda ba ta zuwa wa dan Adam, wani lokaci takan zo a kaikace; wani lokaci kuma a mike. Takan sanya dan Adam kuka, sannan ta sanya shi dariya. Duk wani hali da dan Adam ya shiga kaddara ce daga Ubangiji. Yakan jarraba bawanSa ta hanyoyi da dama…” Na yi shiru, hakan ya sanya ta kalle ni, bayan mun hada idanu ne sai ta sake sunkuyar da kanta. Na kalli Hassan, shi ma ya kalle ni, sai dai har yanzu yana tsaye yana sauraro da ganin wainar da muke toyawa.
“…Don haka nake so ki sanar da ni abin da ya yi ruwa da tsaki wurin kawo ki gidan yari duk da karancin shekarunki.” Na sake yin shiru, sannan na ci gaba da kallonta, ina kuma mayar da numfashi.
Ina kallon lokaci da ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ja dogon numfashi. Hakan ya sanya ni da Hassan muka ci gaba da kallonta, ganin shirun ya tsawaita ne sai na ci gaba da magana: “Tun ranar farko da na gan ki na ji tausayi mai nauyi ya ratsa zuciyata, tun da muka bar gidan yarin nan har zuwa yanzu na kasa samun natsuwa. Ki sani na kasa yin barci mai inganci saboda halin da na gan ki a ciki. Don haka nake bukatar sani dalilin da ya kawo ki gidan yarin nan.”
Ba mu ankara ba sai ganin hawaye muka yi na fitowa daga idanunta, daga bisani ta kwanta a kan teburin da ke tsakiyarmu. Muka ci gaba da kallonta cikin tashin hankali da jimami, hakan ya sanya na ci gaba da yi mata tausasan kalamai masu dauke da rarrashi da kuma ratsi-ratsin tausayi. Daga baya ne hawayen ya daina zubowa daga idanunta. Bayan wani lokaci ne sai ta fara Magana:
“Sunana Hannatu Isma’il (ba sunanta na gaskiya ba), an haife ni a garin Keffi, a yanzu shekarata 19. Abubuwa masu yawa sun faru kafin a yanke mini hukuncin daurin rai-da-rai….”
Don jin yadda za ta kasance sai ku bi mu bashi zuwa wani makon idan Allah Ya kai mu.