Labarin Hannatun Keffi (4)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A makon jiya mun dasa aya a wurin da Hannatu take ba su Bashir labarin dalilin ya sanya aka yanke mata hukuncin daurin rai-da-rai, inda ta ce abubuwa da yawa sun faru kafin a yanke mata hukuncin. A wannan makon za mu ci gaba daga wurin […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A makon jiya mun dasa aya a wurin da Hannatu take ba su Bashir labarin dalilin ya sanya aka yanke mata hukuncin daurin rai-da-rai, inda ta ce abubuwa da yawa sun faru kafin a yanke mata hukuncin. A wannan makon za mu ci gaba daga wurin da muka tsaya. A sha karatu lafiya
“Sunana Hannatu Isma’il (ba sunanta na gaskiya ba), an haife ni a garin Keffi, a yanzu shekarata 19. Abubuwa masu yawa sun faru kafin a yanke mini hukuncin daurin rai-da-rai….” Ta yi shiru, sannan ta fara mayar da numfashi. Ni da Hassan muka ci gaba da kallonta.
“Mahaifina kafin ya rasu makaho ne, ya samu makantarsa ne ta hanyar wani kwaro da ya fada masa ido, inda al’amarin kamar wasa ya yi sanadiyyar makancewarsa, kodayake an alakanta talaucinsa da har ya kasa biyan kudin magani ne ya sanya ya makance. Kafin ya makance faskare da sauran duk aikin karfin da ya samu yake yi. Mahaifiyata masifaffiya ce, ba ta da hakuri, abu kadan ne yake bata mata rai, kuma irin mutanen nan ne masu son kudi. Mu biyu ne ’ya’yansu, ni da kanina Hashim. Tun da na taso ban san karatun boko ko na addini ba, babu irin kokarin da mahaifina bai yi don mu rika zuwa makaranta ba, amma mahaifiyarmu ta yi kememe, a zuwan idan mun je makaranta me za a ci a gidan. Na tuna wata rana da mahaifinmu yake yi wa mahaifiyarmu nasiha a kan muhimmancin ilimi, ai kuwa ta inda ta shiga ba ta nan ta rika fita ba.” Ta sake yin shiru.
“A ranar na yi kwashe, a lokacin da take lakada mini duka ne, sai mahaifina ya shigo gidan, a nan ya rika yi mata magana a kan ta bar duka na, amma ta yi kunnen uwar shegu, ta ci gaba da lakada mini duka, tun ina kuka har na daina, ta ci gaba da lakada mini duka har sai da ta gaji kafin ta bar ni. Daga nan ta rika huci kamar mesa, daga bisani ta ce idan har ba zan mayar da hankali wajen talla ba, to zan ci gaba da yaba wa aya zakinta. Idan zan ci gaba da yi mata kwashe, to jikina zai ci gaba da gaya mini.
“Bayan ta dasa aya ne, sai ta ci gaba da cika da batsewa, har a karshe ta sace gaba daya kamar tayar da ta yi faci. Daga nan cikin murya mai taushi sai mahaifinmu ya fara yi mata nasiha: “Dukan ’ya’ya ba shi ne hanya mafi dacewa ta ba su tarbiyya ba, ki yi musu nasiha mai dauke da nuna masu illa ko amfanin abu ne hanya mafi dacewa. Ki ba su ilimi, kasancewar shi ne gishirin zaman duniya, ko ba ka bar wa danka gadon dukiya ba, idan ka ba shi ilimi, to ka ba shi jarin da zai rika juyawa har ya ci ribar zaman duniya…”
“Ka ce haka mana, me kake tsinana mana a gidan nan? Ban da ka wanke goma ka tsoma biyar babu abin da kake yi. Batun ba da tarbiyya kuwa ai idan amarya ba ta hau doki ba, ai kuwa ba za a dora mata kaya ba. Na yi iya bakin kokarina; na nuna wa ‘ya’yana yadda za su dogara da kansu. Na koya musu sana’a. Ko ba komai sun samu abin da zai taimake su zaman duniya.” Inji mahaifiyarmu, sannan ta ci gaba surutu. Ina kallon lokacin da mahaifina ya yi shiru cikin takaici, wanda bai san lokacin da hawaye ya rika surtu daga idanunsa ba. Ina so na ba shi hakuri amma ina tsoron kada kilu ta ja bau, wato hakan zai iya sake jefa ni cikin wani taskun. Haka ta ci gaba da kwakwazo amma bai ce mata komai ba.” Ta yi shiru, hakan ya sanya na gyara zama. A nan na lura cewa ashe tuni tausayi ya dade da samun nasara a kan Hassan, wanda shi ma na ga ya gyara tsayuwarsa hade da kara tattara hankalinsa gare ta. Daga nan na ce muna sauraronta. Bayan ta mayar da numfashi sai ta ci gaba da ba mu labari:
“Na fara da wannan matashiyar ne don ku gane a wani irin gida na taso. Ban san wani abu da ake kira farin cikin rayuwa ba har sai da na hadu da masoyina Khalid. Na fara haduwa da Khalid ne wata rana ina dauke da kayan talla zan wuce ta karamin shagonsa da yake sayar da kayayyakin masarufi. Sai ya kira ni, ban yi kasa gwiwa ba na nufi wurinsa.
Don jin wainar da za a toya sai ku biyo zuwa mako mai zuwa idan Allah Ya kai mu.