Labarin Hannatun Keffi (5)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna ci gaba da bin mu sau da kafa don jin wainar da ake toyawa a labarin Hannatun Keffi. A makon jiya mun tsaya a wurin da Hannatu ta zuba wa Khalid abinci. A yanzu kuma za mu ci gaba: “Bayan na isa shagonsa […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna ci gaba da bin mu sau da kafa don jin wainar da ake toyawa a labarin Hannatun Keffi. A makon jiya mun tsaya a wurin da Hannatu ta zuba wa Khalid abinci. A yanzu kuma za mu ci gaba:
“Bayan na isa shagonsa ne cikin murmushi da fara’a ya tambaye ni abin da nake sayarwa. Na ce masa gwaten doya da wake, cikin murmushi ya ce mini ya dade bai ci gwaten doya da wake ba. Daga nan ya gaya mini na farashin da zan zuba masa. Na zuba masa, a lokacin da zan mika masa abincin ne ya ciro kudi, a lokaci guda ya miko mini. Ina karbar kudina; yana karbar abincin. Hakan ya sanya muka hada ido, ya sake fadada fuskarsa da murmushi. Ba zan manta da kamshin turarensa da ya bugi hancina ba. Daga nan ya ce mini idan ya ji abincin babu dadi zai karya miki kafa, ya fadi hakan ne cikin sigar wasa, sannan ya fara dariya don ya tabbatar mini da ba ya nufin abin da ya fada ba ne. Ganin haka sai na murtuke fuska. Haka ya sa ya ce “ke saki ranki. Wasa nake yi”, daga nan ya fara cin abincin, “kai wannan abinci haka, ba ki ga kunnena ya fara rawa ba?” Ya tambaye ni cikin sigar zolaya. Na yi dariya. “Ka ji wai dariya take yi, to abincin bai yi dadi ba.” Ya ce da ni ganin ban tamka masa ba, wanda hakan ya na sake murtuke fuska.
“Bayan ya sanya abincin a bakinsa ne sai ya sake yin banza da ni, sannan ya fara kallon wani wuri a cikin shagon nasa. Na ji wani iri, domin tun da na kalle shi na ji zuciyata ta buga, sannan ta ci gaba da saka mini wani abu da na kasa ganewa. A lokuta da dama idan na sanya wa mutum abinci idan har a shago ne ko wani wurin aikinsa nakan tafi, daga baya sai in dawo in dauki kwano ko robata. Amma a wannan karon na kasa aikata hakan. Ganin haka sai ya ce yaya ba zan tafi ba, zan sanya shi a gaba kamar zai gudu.
“Bayan na murguda baki sai na ce “ai da ganin ka idan na tafi to guduwa za ka yi, kasancewar kamanninka duk sun nuna kai ma’abocin gudu ne. Ya daina ci abincin, a lokaci guda ya yi dariya, sannan ya fuskance ni. “Me kike nufi da hakan? Wadanne kamanni ne da ni da suka nuna ni ma’abocin gudu ne?” Ya tambaye ni, sannan ya tsare ni da kallo. Daga nan na ce masa “Ka ga ba surutu na fito ba, yi sauri ka kammala don na dauki robata na wuce.”
“Daga nan sai ya fara dibar abincin kadan-kadan, ya rika yin zai ci kamar ba zai ci ba. Da na fahimci manufarsa sai na fara dariya, sai ya ce “ashe ba za ki ji haushi ba?” Ya tambaye bayan ya ciji lebensa. “Ai tun da na gane kai ma’abocin zolaya ne, to babu abin da za ka yi dada ni da kasa.” Na ba shi amsa. Hakan ya sa ya yi dariya, sannan ya fara cin abincin da sauri-da-sauri. Har ya gama, bai kara ce mini komai ba. Bayan ya kammala cin abincin ne sai ya ci gaba da zolaya, a takaice dai har muka yi sallama bai daina zolayata ba, daga nan ya bukaci na kawo masa abinci gobe.
“A ranar na sayar da abincina da wuri, inda bayan na koma gida ne na samu mahaifiyarmu ba ta lafiya, wanda hakan yake nuna yau ba zan yi abincin dare na sayarwa ba. Murna a wurina kada a tona, sai dai murna ta koma ciki bayan da na kwanta a kan yagalgalalliyar katifata sai na kasa barci. Tunanin Khalid ne ya mamaye kwakwalwata da kuma zuciyata, sai juye-juye nake yi.
Za mu ci gaba in sha Allahu.