Labarin Hannatun Keffi (6)

Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga karshen labarin da muka fara kawo muku makonnin biyar da suka gabata. “Washegari haka kawai na ji ina so lokacin fita ta talla ya yi don na ga Khalid. Bayan na fita ne na bi ta shagonsa, farin cikin da na ga ya shiga bayan […]

Labarin Hannatun Keffi (6)

Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga karshen labarin da muka fara kawo muku makonnin biyar da suka gabata.

“Washegari haka kawai na ji ina so lokacin fita ta talla ya yi don na ga Khalid. Bayan na fita ne na bi ta shagonsa, farin cikin da na ga ya shiga bayan ya gan ni ne ya dada kwantar mini da hankali. Na sanya masa abinci, bayan ya ci ne ya ba ni kudi na ki karba, bayan ya nuna fushinsa ne na ce masa ni ce na ce ya bar shi, bawai roka ya yi ba, daga karshe ya yi godiya. Haka muka ci gaba har daga baya ya furta mini yana so na. Na amince muka ci gaba da soyayya. Daga nan ya nemi izini a gidanmu aka amince masa, sai dai kullum kalubalen da nake fuskanta daga wurin mahaifiyata shi ne in rika tambayarsa kudi.
“Ana cikin haka ne wata rana na kai talla wani wuri da ake gina sabon gida, sai na hadu da Alhaji Ibrahim (Ba ka da sabo), shi ne yake gina sabon gidan, abin mamaki gare ni shi ne, bayan mun hada ido sai na ga yana yi mini kallon so, mamakina ya karu bayan ya aika an kira ni, bayan na zo wurinsa ne ya ce yana so na, na ji abin kamar mafarki. Duk da haka sai da na sanar da shi ina da wanda zan aura. Amma kememe ya ki, a takaice sai da ya yi amfani da kudi wajen cim ma burinsa. Ya saya mana gida, na daina talla, abinci kala-kala ake kawowa gidanmu. Duk da haka sai da na kekasa kasa na fada wa mahaifiyata ba na sonsa. Haka na rika yi masa wulakanci, na yau daban; na gobe da jibi ma daban.
Akwai ranar da na yi masa tatas, ashe mahaifiyata tana labe a lokacin da muke hira. Bayan ya tafi ne ta lakada mini duka. Haka ta rika dukana duk lokacin da na yi wa Alhajin wulakanci, wata rana har ta karya mini hannu. Haka aka yi jinyata har na warke. A takaice Khalid har ofishin ‘yan sanda mahaifiyata ta kai shi a kan wai ya yi mini asiri. Aka lakada masa duka, sannan aka gargade shi kada ya kara kusanta ta. Kafin lokacin babu irin kudin da Alhajin bai nemi ya ba shi a kan ya ce ba ya sona ba, amma ya ki.
A karshe dai haka aka daura mini aure da Alhaji wanda yake ’ya’ya sha takwas da mata biyu ni ce ta uku. Kafin lokacin na yanke shawarar zan gudu, amma Khalid ya hana ni, ya ce hakan ba shi ne mafita ba, kuma ban san wacce irin rayuwa zan fada ba. Mu fawwala Ubangiji komai.
“Bayan an yi auren ne na ci gaba da gallaza masa, amma ya ci gaba da jurewa. A karshe dai wata rana na dafa masa abincin da ya fi so, wato tuwon shinkafa da miyar taushe, sannan na sanya maganin barci, bayan ya ci ne sai barci ya kwashe shi, inda na yi amfani da wuka na yanka shi…” Ta daina ba da labarin, a lokaci guda ta rika kuka. Ni da Hassan muka rika kallonta. Bayan wani lokaci ne, sai ta ci gaba.
“Bayan na yanka shi ne sai tsoro ya kama ni, ai kuwa sai na yi waje da gudu. Washegari labarin mutuwarsa ya cika gari, ni kuma na rika wasan buya har a karshe ‘yan sanda suka kama ni. Shi ne aka yi shari’a har aka yanke mini hukuncin daurin rai-da-rai. Mahaifiyata ta rika tsine mini. Mahaifina ya yi kukan bakin ciki har ciwon zuciya ya kama shi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Daga baya bayan an ci gaba da bincike ne aka gane Alhaji matsafi ne, inda aka samu kawunan mutane uku a wani dakinsa na sirri. Wannan shi ne labarina.”
Ta yi shiru, muka yi shiru kamar ruwa ya cinye mu. Daga baya muka yi sallama. Bayan wata daya ne na koma sai aka sanar mini Hannatu ta rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Mun kammala.
A karshe ina so masu karatu su turo mini darussan da suka koya daga wannan labarin ta wannan lambar 07036925654. Misali: Bashir Musa Liman, daga Abuja, 07036925656, labarin Hannatun Keffi ya koya mini….”