Labarin Hassan mai buhu

Barkanmu da Sallah Manyan Gobe Ina fata kun yi Sallah lafiya, Allah Ya maimaita mana cikin koshin lafiya. A wannan makon Kawunku Bashir Musa Liman ne ya kawo muku labarin Hassan mai buhu. Ina fata Manyan Gobe za ku karanta labarin cikin natsuwa don ku amsa tambayar da ya yi muku a karshen labarin.A sha […]

Labarin Hassan mai buhu
Labarin Hassan mai buhu

Barkanmu da Sallah Manyan Gobe

Ina fata kun yi Sallah lafiya, Allah Ya maimaita mana cikin koshin lafiya. A wannan makon Kawunku Bashir Musa Liman ne ya kawo muku labarin Hassan mai buhu. Ina fata Manyan Gobe za ku karanta labarin cikin natsuwa don ku amsa tambayar da ya yi muku a karshen labarin.
A sha karatu lafiya
Taku: Gwaggwo Amina Abdullahi

Labarin Hassan mai buhu

Daga Bashir Musa Liman

A wani lokaci da ya wuce an yi wani ma’auni da ake kira Hassan, ya mallaki wani buhu mai daukar kwano 8 na masara. Ana cikin haka sai wani ya zo sayen kwano 4 na masara, abin takaicin shi ne Hassan da kuma mai sayen ba su da abin awo sai dai mai sayen ya zo da buhu 2. daya yana cin kwano 5, daya kuma 3.
Manyan Gobe idan ku ne Hassan ta yaya za ku raba kwano 8 na masara ba tare da kun yi amfani da ma’auni ba, sai wadannan buhunhuna 2, sannan kwano 4 na masarar su zama a cikin buhu mai cin kwano 5?
Za ku iya turo amsar wannan tambaya ta wannan lambar: 07036925654