Labarin Hassan mai buhu da kuma amsa

Barka da warhaka Manyan Gobe Yaya hutu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin.Makonnin biyu da suka wuce mun kawo muku labarin Hassan mai buhu, sannan muka nemi ku turo mana da amsar tambayar da muka yi muku. Da farko za mu sake ba ku labarin, musamman idan wadansu bas u […]

Labarin Hassan mai buhu da kuma amsa
Labarin Hassan mai buhu da kuma amsa

Barka da warhaka Manyan Gobe

Yaya hutu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin.
Makonnin biyu da suka wuce mun kawo muku labarin Hassan mai buhu, sannan muka nemi ku turo mana da amsar tambayar da muka yi muku. Da farko za mu sake ba ku labarin, musamman idan wadansu bas u karanta labarin ba, sannan mu yi muku bayanin yadda awun zai kasance. Muna fata za ku bi bayanin sau da kafa.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Labarin Hassan mai buhu da kuma amsa

Daga Bashir Musa Liman

A wani lokaci da ya wuce an yi wani ma’auni da ake kira Hassan, ya mallaki wani buhu mai daukar kwano 8 na masara. Ana cikin haka sai wani ya zo sayen kwano 4 na masarar, abin takaicin shi ne Hassan da kuma mai sayen ba su da abin awo sai dai mai sayen ya zo da buhu 2. daya yana cin kwano 5, daya kuma 3.
Manyan Gobe idan ku ne Hassan ta yaya za ku raba kwano 8 na masara ba tare da kun yi amfani da ma’auni ba, sai wadannan buhunhuna 2, sannan kwano 4 na masarar su zama a cikin buhu mai cin kwano 5?
Amsar labarin:
Mu dauki buhu mai cin kwano 8 ya zama A, buhu mai cin kwana 5 ya zama B, buhu mai kwano 3 kuma ya zama C.
Daga farko a zuba kwano 5 cikin buhu B, saura kwano 3 cikin buhu A, buhu C kuma zai zama babu komai a ciki. Daga nan sai a zuba mudu 3 a cikin buhu C daga cikin buhu B, kun ga saura mudu 3 a cikin buhu A, mudu 2 a cikin buhu B, mudu 3 kuma a cikin buhu C.
Dawo da mudu 3 daga buhu C zuwa buhu A, a lokaci guda debi mudu 2 daga buhu B zuwa C. Idan an yi hakan zai zama an samu mudu 6 a buhu A, mudu 2 a buhu C, buhu B kuma zai zama babu komai a ciki.
Daga nan sai a debi mudu 5 daga buhu A sannan a zuba cikin buhu B, don haka mudu 1 zai rage a buhu A, mudu 5 a buhu B, mudu 2 kuma a buhu C.
Tun da buhu C ba zai dauki fiye da mudu 3 ba, kuma a yanzu na dauke da mudu 2 ne, don haka saura mudu 1 ya cika. Idan haka ne sai mu diba daga buhu B a cika buhu C. Idan an yi hakan sai buhu C ya zama mudu 3, shi kuma buhu B ya zama mudu 4, kuma da ma an ce ana so mudu 4 ya zama a cikin buhu mai cin mudu 5.