‘Labarin Jemage’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku ‘Labarin Jemage’ labarin ya kunshi yadda yawan sauraro yafin yawan surutu. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Akwai wani jemage a wata bishiya a wani kauye. Shi dai a kullum ba ya magana sai dai ya yi ta sauraro. […]

‘Labarin Jemage’
‘Labarin Jemage’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku ‘Labarin Jemage’ labarin ya kunshi yadda yawan sauraro yafin yawan surutu. A sha karatu lafiya.

Taku: Amina Abdullahi

Akwai wani jemage a wata bishiya a wani kauye. Shi dai a kullum ba ya magana sai dai ya yi ta sauraro. Rannan ya ga wata mata ta zo wucewa da kaya a kanta, sai danta ya karba ya daura a kansa. Washegari kuma ya ga wata yarinya karama wadda mahaifiyarta ta haifeta ta ki zuwa.
Sakamakon rashin surutunsa ya sa ya zama mai wayo. Wata mata tana ta yada wani labari wai giwa ta tsallaka katanga da gudu.
Shi dai baya fadin komai sai dai ya saurara. Ana cikin hakan kwatsam sai ya samu labarin cewa a kashe duka jemagen da ke garin.
Aiko bai yi wata-wata ba ya tashi daga kan wannan bishiyar ya koma zama a daji.
Toh Manyan Gobe, da jemage dai ya kasance mai yawan surutu da ba zai samu labarin kisan ba. Don haka ina son Manyan Gobe su dau darasi su zama masu yawan sauraren magana a maimakon surutu domin yin hakan yana kara basira.