Labarin Kare da Kyanwa

Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘kare da kyanwa’. Labarin ya kunshi yadda wata rana makiyi zai iya zama aboki na hakika. A sha karatu lafiya:A wani kauye ne Kare ya gayyaci abokinsa Kyanwa zuwa wata walimar da ya shirya. Da […]

Labarin Kare da Kyanwa
Labarin Kare da Kyanwa

Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘kare da kyanwa’. Labarin ya kunshi yadda wata rana makiyi zai iya zama aboki na hakika. A sha karatu lafiya:
A wani kauye ne Kare ya gayyaci abokinsa Kyanwa zuwa wata walimar da ya shirya. Da kyanwa ta isa sai ta fara yin kidi sai Kare ya shiga yin rawa yayin da sauran dabbobin sai kallonsu suke abin ya ba su mamaki  ganin yadda suka shaku da juna bayan an sha jin kansu.
Ashe kare ya yi niyyar hadawa kyanwa tarko ne.   Suka cigaba da kide-kide da raye-rayensu. Kawai tarkon da aka hada wa kyanwa ya kama wata saniya.  Nan kare ya shiga yin murna cewa sun samu isasshen naman da zai ishi duk bakin da ya gayyto maimakon tarkon ya kama kyanwa da ba ta da girma ya samu nasarar kama babban nama, wato saniya.
Nan da nan aka dora sanwa aka shiga girki da suya naman saniya da ya cika kwano.  Amma ganin yadda kyanwa ta dage wajen tafiyar da harkokin girkin ne ya sa kare ya shiga jin tausayinta.  Nan take ya fadawa kyanwa burinsa na kokarin halakata a baya, amma yanzu ya gane kurenasa kuma nan take ya nemi gafarar kyanwa, ita kuma ta gafarta masa.  Daga nan abota ta sake kulluwa inda suka zama aminan juna.
Ina fata Manyan gobe kun ilimantu da darasin da ke cikin wannan labari inda makiyan juna suma zama aminai.
Sai mako na gaba insha Allah.