Labarin Kunkuuru mai kwadayi
Barka da warhaka Manyan Gobe Da fatan kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo maku labarin Kunkuru, wanda yake kunshe da dalilin da ya sa ya kasance ba shi da gashi. Labarin na kunshe da yadda Manyan Gobe za su koyi hali nagari ba na sace-sace ba. A sha karatu lafiya.Taku : Gwaggo […]
Barka da warhaka Manyan Gobe
Da fatan kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo maku labarin Kunkuru, wanda yake kunshe da dalilin da ya sa ya kasance ba shi da gashi. Labarin na kunshe da yadda Manyan Gobe za su koyi hali nagari ba na sace-sace ba.
A sha karatu lafiya.
Taku : Gwaggo Amina Abdullahi
Labarin Kunkuuru mai kwadayi
A wani gari mai suna Famfam an yi wani kunkuru mai masifar kwadayi. Rannan sai ya je gidansu maman Jummai mai dafa abinci, sai ya samu an girka fate-fate. Sai aka tambayi kunkuru “me za a ba ka?” Sai ya ce kawai dai ya zo ya taya su hira ne.
Jim kadan, sai ta yi baki, sai ta ba kunkuru umarnin ya kula mata da abincin. Sai ya shiga wurin da take ajiye faten. Ya sha na sha sai ya zuba sauran a hularsa domin kada a gano shi. Sai zafin faten ya kone masa gashin da ke jikinsa. Da mai abinci ta zo sai ta ce, ya ta ga faten har ya kare ko an yi ciniki ne? Can sai kunkuru ya fara tsalle hakan aka gano inda ya zuba sauran fate-fate.
Ina fatan Manyan Gobe ba za su rika daukar abin da ba a ba su ba.