Labarin Kura da Bijimi

Barka da warhaka Manyan Gobe Yaya hutu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya.A wannan makon na taho muku da labarin kura da bijimi. Labarin yana kunshe da wani babban darasi. Ina fata za ku bi labarin don ku gano darasin da yake kunshe cikinsa.A sha karatu lafiya.Naku: Kawu Bashir Musa Liman Labarin Kura da Bijimi […]

Labarin Kura da Bijimi
Labarin Kura da Bijimi

Barka da warhaka Manyan Gobe

Yaya hutu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya.
A wannan makon na taho muku da labarin kura da bijimi. Labarin yana kunshe da wani babban darasi. Ina fata za ku bi labarin don ku gano darasin da yake kunshe cikinsa.
A sha karatu lafiya.
Naku: Kawu Bashir Musa Liman

Labarin Kura da Bijimi

A wani zamani da ya shude an yi lokacin da kura ta shiga halin kaka-ni-kayi, saboda ba ta da abin da za ta ci. Rayuwarta ta shiga kunci, ta kuma rasa inda za ta sa kanta.
Da ta ga babu sarki sai Allah sai ta shiga cikin dajin, amma ga mamakinta ba ta hadu da naman dajin da za ta iya kashewa ba, kasancewar ta hadu da bauna da mugun dawa da giwa da damisa da sauransu ne.
Haka ta sanya ta yanke kauna da samun na kalaci, amma a lokaci guda tsumagiyar kan kanya ta ci gaba da ba ta kashi.
Ta kusa dawowa gidan ke nan sai ta hango wani katon bijimi na kiwo, a lokaci guda yana harbin iska.  Ta kare masa kallo, inda kuma yawu ya taru a bakinta. Ta yi yunkurin afka masa ke nan sai ta tuna da murdaddun kahonninsa, bugu da kari ta sha jin labarin yadda yake bugawa da sauran namun daji kuma ya yi nasara a kansu.
Wannan tunani da ta yi sai gwiwarta ta yi sanyi, daga nan ta yi shiru hade da tunanin wace hanya za ta bi don ya samu nasara a kan bijimi. Ana cikin haka sai dabara ta fado masa.
Cikin salama ta sami bijimi a lokacin da yake kiwo. Ga abin da ta ce masa: “Kana da kira mai kyau, ga tozonka abin burgewa, fatarka fara sol abin yabawa, ga ka kosasshe…”
Bijimi ya yi murmushi, sannan ya ci gaba da kallonta, ganin hakarta ta fara cim ma ruwa sai ta ce “…amma abu daya ne ya bata ka.” Bijimi ya bata rai. “…Ba wani abu ba ne illa kahonninka. Da a ce za ka cire su, ai da duk fadin dajin nan babu wanda zai kai ka kyau.” Ta yi shiru, sannan ta ci gaba da kallonsa.
Bijimi ya yi shiru bai ce komai ba, daga nan sai ta hango wata korama, sai ta ce masa su je wurin koramar don ya ga yadda kahonninsa suke sanya shi muni. Ta yi gaba, sannan bijimi ya bi ta a baya. Bayan sun karasa wurin koramar ne sai bijimi ya fahimci abin da take fada masa. A nan ya ji takaici ya kama shi, sannan ya nemi ko za ta iya taimaka masa, don ya cire su.
Ta yi dariyar mugunta a cikin zuciyarta, sannan ta ce ai babu komai duk wanda ya taimaki wani Allah Zai taimake shi.
A karshe dai suka fitar da kahonnin, inda kuma bijimi ya fahimci mummunar manufar kura, a lokacin kuma ba shi da tsimi bare dabara na kare kansa. Haka ta cinye shi.