Labarin kyanwa mai kararrawa
Barka da warhaka Manyan Gobe Fatan alheri a gare ku. A yau na kawo muku Labarin kyanwa mai kararrawa. Labarin na kunshe ne da yadda shawara marar kwari ba ta cika amfani ba. A sha karatu lafiya.Taku; Gwaggo Amina Abdullahi Labarin kyanwa mai kararrawa An yi wani manomi wanda yake da shagon hatsi. Yana da […]
Barka da warhaka Manyan Gobe
Fatan alheri a gare ku. A yau na kawo muku Labarin kyanwa mai kararrawa. Labarin na kunshe ne da yadda shawara marar kwari ba ta cika amfani ba.
A sha karatu lafiya.
Taku; Gwaggo Amina Abdullahi
Labarin kyanwa mai kararrawa
An yi wani manomi wanda yake da shagon hatsi. Yana da kowane nau’in hatsi. Abin yake damunsa shi ne beraye sun dame shi da barna. Kuma suna jawo masa asara. Hakan ya sa ya sayo kyanwa domin ta kula masa da hatsinsa. Kyanwa ta takura wa berayen da ke shagon manomin, domin babu wanda zai yi kwakkwaran motsi ba tare da ta kai masa hari ba.
Sai suka yanke shawara a kan cewa ya kamata su sanya wa kyanwar kararrawa a duk lokacin da za ta wuce, sai su rika jin kararta. Bayan sun gama yanke shawarar, sai daya daga cikinsu ya ce: “wa ye zai sanya wa kyanwar kararrawa?”, suka yi shiru daga karshe aka rasa wanda zai sanya mata. A haka har kyanwar ta cinye su.
Ina fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labarin. Da sun yanke shawara mai ma’ana da kyanwar ba ta samu damar cinye su gaba daya ba.