‘Labarin Mai Faskare’

Barka da warhaka Manyan Gobe Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Na kawo muku ‘Labarin Mai faskare’. Labarin na kunshe da yadda Manyan Gobe za su zamo masu zurfin tunani. Da fatan Manyan Gobe za su nazarci wannan labarin don cin ribar darussan da yake koyarwa.A sha karatu lafiya.Gwaggonku: Amina Abdullahi ‘Labarin Mai Faskare’ An […]

‘Labarin Mai Faskare’
‘Labarin Mai Faskare’

Barka da warhaka Manyan Gobe

Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Na kawo muku ‘Labarin Mai faskare’. Labarin na kunshe da yadda Manyan Gobe za su zamo masu zurfin tunani. Da fatan Manyan Gobe za su nazarci wannan labarin don cin ribar darussan da yake koyarwa.
A sha karatu lafiya.
Gwaggonku: Amina Abdullahi

‘Labarin Mai Faskare’

An yi wani mai faskare da ya samu aiki a wurin wani Alhaji. Ana biyansa albashi mai tsoka. Don hakan, sai ya dage wurin aikin faskarensa.
Ranar farko, sai ya sare bishiya sha takwas (18).  A rana ta biyu kuma sha biyar (15); rana ta uku kuma goma (10). Haka dai bishiyoyin da yake sarewa suka rika raguwa.
Da mai faskare ya ga hakan, sai  ya ji tsoron kada Alhaji ya kore shi, sai ya gaya wa Alhaji yana ganin kullum karfinsa raguwa yake yi. Sai Alhaji ya ce da shi: “Yaushe ka wasa gatarinka tun da ka fara aiki?” Sai mai faskare ya ce “Ai ina faman kokarin aiki na manta ban wasa shi ba.”
A rayuwa ya kamata mu sani cewa, duk yadda muka kai ga kwazo wurin aiki, to ana bukatar mu zamo masu zurfin tunani. Da fatan Manyan Gobe za su zama masu zurfin tunani a kan kowane irin aiki suke yi. Kada su zama masu saurin yanke shawara.