Labarin Manomi da Tsuntsaye

Barka da warhaka Manyan GobeBarkanmu da warhaka Manyan Gobe. Ina fata kuna cikin koshin lafiya, kuma ina fata kun dawo daga hutu lafiya. A yau na kawo muku labarin Manomi da Tsuntsaye. Labarin ya ginu bisa irin abokai da ya kamata Manyan Gobe ku rika yi don ku samu shaida mai kyau. Labarin Manomi da […]

Labarin Manomi da Tsuntsaye
Labarin Manomi da Tsuntsaye

Barka da warhaka Manyan Gobe
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Ina fata kuna cikin koshin lafiya, kuma ina fata kun dawo daga hutu lafiya. A yau na kawo muku labarin Manomi da Tsuntsaye. Labarin ya ginu bisa irin abokai da ya kamata Manyan Gobe ku rika yi don ku samu shaida mai kyau.

Labarin Manomi da Tsuntsaye
Akwai wani manomi wanda kullum tsuntsaye ke yi masa barna a gona. Ga shi kuma abin ya dame shi. Rannan ya sa tarko a gonarsa.
Washe gari, sai ya je gonarsa don ya ga irin tsuntsayen da ke masa barna a gona. Bayan ya je gonar ne, sai ya ga tsuntsaye masu yawa a cikin tarko.
Daga nan sai ya yanke shawarar ya kashe su. Nan take sai daya daga cikin tsuntsayen ya fara kuka yana cewa: “Don Allah ka sake ni, wallahi ban ci maka hatsi ba, kuma ban yi maka barna a gona ba, ni dan kirki ne, kuma ina ba iyayena girmansu, na bi su yawo ne kawai domin su abokaina ne…”
Sai manomi ya katse shi ya ce “Yi mana shiru! Zai yiwu kana da gaskiya amma kuma ai na kama ka tare da masu yi mini barna a gona. Saboda haka sai na halaka ka da wadanda na kama ku tare.” Haka manomi ya halaka su ba tare da ya cire shi ba.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi a cikin wannan labarin. Kuma za su san irin abokan da za su rika ma’amula da su domin an ce ‘abokin barawo, barawo  ne.’